A baje ta a faifai: Gwamnatin Buhari za ta fara wallafa kudin dake shigo mata da wanda take kashewa a kullum a yanar gizo

A baje ta a faifai: Gwamnatin Buhari za ta fara wallafa kudin dake shigo mata da wanda take kashewa a kullum a yanar gizo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci babban akanta na kasa daya dinga bayyana ma yan Najeriya adadin kudaden da suke shiga lalitar gwamnatin tarayya da wanda ke fita daga lalitar a kullum.

Shugaba Buhari ya bada wannan umarni ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba yayin taron kaddamar da dokoki da tsare tsaren fayyace hada hadar kudi na gwamnatin tarayya, inda ya umarci babban akantan ya wallafa rahoton duk wani kudi da aka baiwa kowacce hukuma da ma’aikata daya haura naira miliyan 10.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram rakiyar Kura, sun ceto mata da kananan yara

Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin karamin ministan Neja Delta, Tayo Alasoadura yace rahoton ofishin babban akantan Najeriya ne zai dinga sanar da yan Najeriya adadin kudaden da gwamnati ta baiwa hukumominta da ma’aikatunta domin su gudanar da ayyuka, da kuma sanin adadin kudin daya shigo musu.

Wakilin Buhari yace manufar tsarin shi ne baje ta a faifai kowa ya gani tare da yin keke da keke harkar tafiyar da kudaden al’umman Najeriya ba tare da wani boye boye, kumbuya kumbuya, lumbu lumbu ko muna muna ba.

Bugu da kari, shugaban kasa yace bayanin da za’a dinga wallafawa zai kunshi musabbabin bayar da kudin ko kashe kudin, adadin kudin da kuma wanda ya biya kudin ko aka biya kudin, sa’annan sabon tsarin ya tilasta ma hukumomi da ma’aikatu su tabbatar da wallafa duk wata harkallar kudi data haura naira miliyan 5.

Haka zalika Buhari ya umarci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su wallafa yanayin aiwatar da kasafin kudinsu a kowanne kwanaki 7 na karshen kowanne wata, inda bayaninsu zai hada da ayyukansu da kuma amfanin da suka kara ma tattalin arzikin kasar.

Baya ga wallafa kudaden da suka shigo ma gwamnati da wanda suka kashe, shugaba Buhari ya umarci babban akanta na kasa ya dinga wallafa matsayin asusun gwamnati bayan kowanne watanni 4, sa’annan a karshen shekara ma haka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel