Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram rakiyar Kura, sun ceto mata da kananan yara

Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram rakiyar Kura, sun ceto mata da kananan yara

Akalla dan Boko Haram daya ne ya gamu da ajalinsa a sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin dakarun rundunar Sojin Najeriya tare da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a jahar Borno.

Jami’in kula da watsa labaru na Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba inda yace an yi dauki ba dadin ne a kauyen Malam Fatori cikin karamar hukumar Abadam na jahar Borno.

KU KARANTA: Tsofaffin gwamnoni 9 da EFCC ke zarginsu da satar kudi, amma har yanzu shiru kake ji

Kanal Aminu yace dakarun runduna Soja ta 68/94 ne suka kaddamar da samame a mafakar yan ta’addan Boko Haram dake kauyen, wanda hakan yasa bayan sun sha wuta yan ta’addan suka ranta ana kare, amma Sojoji basu kyalesu, sai da suka musu rakiyar Kura.

A yayin da Sojojin suka fatattaki yan ta’addan ne suka gano gawar dan Boko Haram guda daya, sa’annan sun ga jini nata kwarara a kan hanyar, wanda hakan ke nuna wasu daga cikin yan ta’addan sun tsere da munanan rauni kenan.

Daga cikin makaman da yan ta’addan suka zubar akwai rakumi guda 1, kayan sawa, kayan barci, kayan girke girke, kayan abinci, sassan jikin babur, tukunyar iskar gas guda 122 da dai sauran karafan kera bamabamai.

A hannu guda kuma, Sojoji sun kaddamar da wani samame a mafakar Boko Haram dake kauyukan Mantari, Malam Masari da Gabchari a ranar 4 ga watan Disamba, inda suka kashe dan ta’adda 1, suka raunata wasu da dama, tare da ceto mata 14 da kananan yara 17.

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa, UAE, wanda aka fi sani da Dubai, domin gabatar da jawabi a kan muhimmancin addini wajen hada kan jama’a.

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, inda yace Osinbajo zai gabatar da jawabi a yayin taron ne a matsayin babban mai gabatar da jawabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel