Dole dukannin Malaman Jami’o’i su shiga tsarin IPPIS – Shugaba Buhari

Dole dukannin Malaman Jami’o’i su shiga tsarin IPPIS – Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama dole Ma’aikatan Jami’o’i su yi hijira zuwa tsarin biyan albashi na IPPIS domin tabbatar da gaskiya wajen biyan ma’aikatan.

Muhammadu Buhari ya yai wannan jawabi ne ta bakin Sakataren hukumar TETFund mai kula da cigaban makarantun gaba da sakandare a wajen taron yaye ‘Daliban jami’ar tarayya da ke Jos.

Farfesa Suleiman Elias Bogoro ya yi jawabi a madadin shugaban kasar inda ya fadi fa’idar shiga cikin tsarin albashi na IPPIS. Farfesan ya ce tsarin zai taimaka wajen kashe kudi ke-ke-da-ke.

A cewar Suleiman Elias Bogoro, tsarin IPPIS ya na cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin maganin rashin gaskiya a manyan makarantu na gaba da sakandare da ke fadin kasar.

KU KARANTA: Buhari ya tsige Shugaban hukumar TETFund, Abdullahi Bichi

Daily Trust ta ce Farfesa Bogoro ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke jawabi a matsayin babban bako a wajen bikin yaye ‘Daliban jami’ar UNIJOS da ake shirya a cikin karshen makon jiya.

Bagoro wanda ya koma hukumar TETFund a farkon 2019 ya ba jam’o’i shawara su kara kokarin bada ilmi mai nagarta ta yadda Daliban Najeriya za su iya shiga ko ina a Duniya a kara da su.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta rantse a kan cewa sai Ma’aikatan jami’o’i sun shiga tsarin IPPIS ko kuma a dakatar da albashinsu. A na ta bangaren, kungiyar ASUU ta ce sam ba za ta amince ba.

Shugaban ASUU na reshen Jami’ar UI, Farfesa Deji Omole, ya karyata ikirarin gwamnatin tarayya na cewa Ma’aikata 39, 000 sun shiga IPPIS. Omole ya ce 90% na ‘Ya ‘yan ASUU ba su yi rajistar ba,

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel