'Yan bindiga sun yi wa filin kwallo zobe, sun halaka 'yan kallo 4 a Kaduna

'Yan bindiga sun yi wa filin kwallo zobe, sun halaka 'yan kallo 4 a Kaduna

An ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga dadi sun zagaye filin kwallo inda suka kashe mutane hudu tare da raunata wasu hudu a kauyen Zunuruk na karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito, maharan sun kai harin ne a ranar Lahadi da yammaci yayin da ake wasan kwallon kafa a fili. Maharan sun dinga harbi ta ko ina ne ga masu kallon.

Amma kuma, har yanzu hukumar 'yan sandan jihar Kaduna bata tabbatar aukuwar lamarin ba. Wani ganau ba jiyau ba, wanda ya bukaci da a sakaya sunansa, yace maharan sun bullo ne ta dajin da ke gefen filin kwallon inda suka fara harbin masu kallon ba zato balle tsammani.

DUBA WANNAN: Kalaman kaskanci a kan arewa: Gwamna Matawalle ya yi wa Rochas 'wankin babban bargo'

Majiyar ta ce, wannan harin kuwa ya kawo karshen wasan kwallon kafan, domin kuwa masu kallo da 'yan kwallon sun gudu don tseratar da rayukansu.

Majiyar ta kara da bayyana cewa, a wani kauye mai suna Tsonje da ke da makwabtaka da garin, a safiyar Lahadi ne 'yan kauyen suka tashi da alhinin ganin gawar wani mutum da suke zargin an kashesa ne da bindiga. Wannan zargin kuwa ya biyo bayan ganin gawarsa da aka yi da harbin bindiga.

Mamacin wanda aka bayyana da suna Dogara Kazzah, an ruwaito cewa ya je fitsari ne a dajin da ke gefen kauyen da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar. Amma kuma bai koma gida ba, sai tsintar gawarsa da aka yi a safiyar ranar Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel