Buhari ya canja Fowler, ya nada Muhammad a matsayin shugaban FIRS

Buhari ya canja Fowler, ya nada Muhammad a matsayin shugaban FIRS

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Muhammad M. Nami a matsayin shugaban FIRS

- An gano cewa, Nami zai maye gurbin Tunde Fowler ne wanda wa'adin mulkinsa ya cika a ranar Litinin da ta gabata

- Sabon shugaban hukumar, kwararre ne a bangaren haraji kuma ya kammala karatunsa ne a jami'ar Ahmadu Bello

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Muhammad M. Nami a matsayin shugaban hukumar kudin shiga ta tarayya, FIRS.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Nami zai maye gurbin Tunde Fowler, wanda wa'adin mulkinsa ya kare a ranar Litinin da ta gabata.

Sabon shugaban hukumar, kwararre ne a bangaren haraji kuma ya kammala karatunsa ne a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

DUBA WANNAN: Kalaman kaskanci a kan arewa: Gwamna Matawalle ya yi wa Rochas 'wankin babban bargo'

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun shugaban kasan, Garba Shehu, tace: "Muhammad kwararre ne a bangaren haraji, kididdiga da lissafi kuma gogagge ne a shugabanci. Yana da kwarewa tare da gogewa. Ya mallaki lasisin aiki daga cibiyoyi majibanta kuma ya yi a kalla shekaru 30 yana aiki a bangarorin haraji, shugabanci da kididdiga. Ya yi aiki a cibiyoyin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba,"

Kamar yadda Shehu ya sanar, shugaban kasan ya aminta da hadin kungiyar shugabancin FIRS din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel