Za mu cigaba da biyan Orji Uzor Kalu albashi da alawus a Kurkuku - Majalisar dattawa

Za mu cigaba da biyan Orji Uzor Kalu albashi da alawus a Kurkuku - Majalisar dattawa

- Mai magana da yawun majalisar dattawar Najeriya, Godiya Akwashiki, ya bayyana cewa har yanzu Sanata Orji Kalu zai samu albashi duk da cewa an jefashi kurkuku

- Akwashiki ya ce har yanzu Orji Uzor Kalu Sanata ne mai ci

- Ya ce ba za'a daina biyansa ba sai kotun koli ta yanke hukunci na karshe kan lamarin

Majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa Sanata Orji Uzor Kalu zai cigaba da samun cikakken albashinsa da alawus-alawus duk da cewa kotu ta yanke masa hukuncin gidan yarin shekara 12.

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Godiya Akwashiki, ya bayyanawa Premium Times ranar Lahadi, 8 ga Disamba cewa za'a biya Orji Kalu dukkan hakkokinsa saboda har yanzu Sanata ne mai ci.

Ya ce ba za'a gushe ana ganinsa matsayin Sanata ba har sai lokacin da lamarinsa ya kai kotun koli kuma aka yanke hukunci.

Akwashiki yace: "Har yanzu Sanata. Wannan kotun farko ne. Lamarin zai kai kotun koli, har yanzu yana da daman daukaka kara har kotun koli."

"Ko shakka babu za'a biyashi. Saboda har yanzu Sanata ne kamar yadda na fada.... Idan ka daukaka kara, har yanzu kana kujerarsa saboda haka zasu biya ka."

A yanzu dai, Orji Uzor Kalu yana Kurkuku kuma yana shirin komawa kotu domin samun beli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel