Daliban sakandari sun karya malaminsu bayan sun sha kwaya sun yi mankas

Daliban sakandari sun karya malaminsu bayan sun sha kwaya sun yi mankas

Daliban sakandari na makarantar Zappa dake garin Asaba na jahar Delta sun lakada ma wani Malaminsu dan banzan duka sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi da suke yi, inda suka sha suka yi mankas!

Jaridar Punch ta ruwaito daliban sun aikata ma malamin wannan aika aika ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan kammala jarabawar zangon karatu na farko, inda suka tare malamin yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida.

KU KARANTA: Osinbajo ya tafi kasar Dubai domin ganawa da yariman kasar mai jiran gado

Daliban sakandari sun karya malaminsu bayan sun sha kwaya sun yi mankas

Daliban sakandari sun karya malaminsu bayan sun sha kwaya sun yi mankas
Source: Facebook

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ba tare da wata wata ba aka garzaya da malamin zuwa cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya dake garin Asaba domin bashi kulawa sun karya masa kashin goshi.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito an yi sa’a jami’an Yansanda dake yankin sun samu nasarar kama wasu daga cikin daliban a cikin harabar makarantar.

Haka zalika wani dan rajin kare hakkin bil adama, Victor Ojei ya bayyana damuwarsa game da yadda shaye shaye ke lalata tarbiyyar yara a jahar Delta, musamman daliban sakandari. A cewarsa: “Yaran sun kai ma malaminsu hari, kuma an garzaya da shi FMC domin samun kulawa.

“Yanzu dalibai sun rungumi shaye shayen kwayoyi a jahar Delta, babu irin kwayar da yaran nan basa sha, yanzu ga irinta nan sun fasa masa goshi.”

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa, UAE, wanda aka fi sani da Dubai, domin gabatar da jawabi a kan muhimmancin addini wajen hada kan jama’a.

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, inda yace Osinbajo zai gabatar da jawabi a yayin taron ne a matsayin babban mai gabatar da jawabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel