Muhammadu Sanusi II ne Shugaban Sarakunan Kano – Gwamna Ganduje

Muhammadu Sanusi II ne Shugaban Sarakunan Kano – Gwamna Ganduje

Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya zabi Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ya jagoranci majalisar Sarakunan kasar Kano. Daily Trust ta rahoto wannan dazu nan.

Abdullahi Ganduje ya nada Sarkin Birni, Malam Muhammadu Sanusi II a kan kujerar Shugaban Sarakunan jihar. Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Ganduje ta kafa wasu sababbin Masarautu.

A wani jawabi da ya fito ta bakin babban Sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya bayyana cewa nadin ya dogara ne da sashe na 4(2) (g) da sashe na 5(1) (2) na dokokin masarauta.

A dokar masarauta da aka rattabawa hannu a shekarar nan ta 2019, an ba gwamna damar nada Sarkin da zai jagoranci zaman sauran Sarakunan da ke karkashin majalisar Sarakuna ta jihar.

KU KARANTA: Malami ya ce bai dace Gwamnan Kano ya wargaza tsarin Sarakuna ba

Wannan nadi da aka yi wa Sarkin Birni, Muhammadu Sanusi II, ya fara aiki ne daga yau Ranar Litinin 9 ga Watan Dimsaban 2019. Kwana biyar kenan bayan an sa hannu a dokar masarauta.

Jawabin Sakatarem yada labaran ya bayyana cewa Mai girma gwamna ya umarci Mai martaba Sanusi II ya yi maza ya kira taron farko na Sarakunan jihar kamar dai yadda doka ta tanada.

Sauran Sarakunan na Kano su ne Alhaji Aminu Ado Bayero na Bichi, Dr. Tafida Abubakar na Rano, da Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir, sai kuma Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II.

Gwamna ya bada duka wadannan sababbin Sarakuna daraja ta farko. Sauran ‘Yan majalisar sun hada da SGF, Kwamishinan kananan hukumomi, da wasu wakilan gwamnatin jiha da Malamai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel