Tinubu ya kamata ya karbi Buhari - Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas

Tinubu ya kamata ya karbi Buhari - Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas

Wata kungiyar siyasa ta Matasan Yankin Arewa maso Gabas mai suna “North Eastern Youth Mobilization Congress” ta soma yi wa Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu mubaya’a.

Wannan kungiyar ta Arewa ta nuna cewa babu wanda ya dace da Najeriya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a shekarar 2023 irin tsohon gwamna Bola Tinubu.

Kungiyar ta bayyana goyon bayan ta ne a karshen makon nan wajen kaddamar da sababbin shugabanninta a jihar Bauchi. Shugaban kungiyar, Aliyu H. Balewa ya fito ya bayyana wannan.

Daily Trust ta ce a jawabin, Balewa, ya nuna cewa makasudin wannan kungiya ta su ta North Eastern Youth Mobilization Congress shi ne karfafa abokantaka tsakanin ‘yan siyasar kasar nan.

Kungiyar ta na ganin wannan dankon zumunci ne zai kawo zaman lafiya da cigaba a Najeriya. Wannan ya sa kungiyar ta fara hangen wayewa da kishin kasa da sanin siyasar Tinubu.

KU KARANTA: Bai kamata ace dole sai ‘Dan Arewa zai yi mulki a 2023 ba - Gumi

Aliyu Balewa ya na kuma ganin Bola Tinubu a matsayin Malamin siyasa da ya bada gudumuwa sosai wajen nasarar jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari a zabukan 2015 da 2019.

Wannan kokari na Jagoran jam’iyyar ya sa Balewa ya ke ganin ya kamata a ba shi tikitin takarar shugaban kasa a APC a 2023. Bugu da kari, kungiyar ta ce Tinubu cikakken ‘dan kishin kasa ne.

A lokacin da Tinubu ya ke mulki, ya jawo mutanen wasu jihohi a gwamnatinsa inji Mista Balewa, don haka ya ke kira a yi adalci wajen ganin mulki ya koma Kudancin Najeriya bayan Buhari.

Shugabannin da kungiyar ta nada su ne: Aliyu H. Balewa, Muhammad Ibrahim B, Umar Alhaji, Abdullahi Ya’u Mai Fure, M.A Almustapha, Anas Abubakar, da Abdulrashid Haruna Gombe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel