Lalata da dalibi mai shekaru 6: Gwamna Buni ya dakatar da basarake a Yobe

Lalata da dalibi mai shekaru 6: Gwamna Buni ya dakatar da basarake a Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da Dagaci Lawan Fannami na karamar hukumar Bade da ke jihar Yobe a kan luwadi da yaro dan makaranta mai shekaru 6 kacal a duniya. Basaraken ya dau a kalla shekara daya yana lalata da yaron.

A takardar da kwamishinan yada labarai, al'amuran cikin gida da al'adu na jihar ya fitar, Gwamnan ya bada umarnin daukan matakin bincike tare da hukunta basaraken a kan wannan laifin.

"A halin yanzu, basaraken da abun ya shafa an dakatar dashi daga shugabantar gundumar Fannami a Gashua har zuwa lokacin da jami'an 'yan sanda zasu kammala bincike a kan lamarin.

"An aike da wasika kunshe da wannan bukatar ga shugaban karamar hukumar Bade ta jihar. Shi kuma yaron da aka yi wa fyaden, an mikashi ga masana kiwon lafiya inda suka dubashi tare da bashi taimakon da ya kamata a babban asibitin Gashua," in ji takardar.

DUBA WANNAN: Kada ka gurbata tarihin sama da shekaru 1000 - Dattijan Kano sun gargadi Ganduje

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, lamarin ya fara ne a shekarar da ta gabata. Basaraken ya tsayar da yaron da ke kan keke a hanyarsa ta zuwa makaranta. Ya yaudaresa zuwa cikin daki inda ya yi masa fyade.

"Ba sau daya ba, ba sau biyu ba Lawan ya yi luwadi da karamin yaron. Ya yaudari yaron ne zuwa cikin daki a yayin da yake wucewa a kan keke zuwa makaranta," wani makwabcinsu mai suna Sale Modu ya sanar da jaridar Daily Nigerian.

"Mahaifin yaron ne ya hanzarta mika shi asibiti bayan da ya gano ciwuka da jini ta duwawun yaron. A asibitin ne aka bayyana gaskiyar abinda ya faru da yaron.

"Yaron ya boye wa iyayensa mummunan lamarin da ke faruwa dashi sama da shekara daya. Hakan ya biyo bayan barazanar kashesa da basaraken yake yi matukar ya sanar da wani." cewar makwabcin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel