Fadar Shugaban kasa ta sa bakinta a cikin rikicin Yele Sowore da Hukumar DSS

Fadar Shugaban kasa ta sa bakinta a cikin rikicin Yele Sowore da Hukumar DSS

Fadar Shugaban kasa ta yi magana wannan karo a game da sake cafke Omoyele Sowore da hukumar DSS ta yi. Garba Shehu ne ya fitar da wani dogon jawabi a Ranar 8 ga Watan Disamba.

“Fadar Shugaban kasa ta fahimci abin da wasu ke rayawa a game da cafke Omoyele Sowore da jami’an DSS su ka yi. Hukumar DSS ba ta bukatan umarnin shugaban kasa wajen duk ayyukanta.”

“Nauyin da ya rataya a kan DSS ya na cikin kundin tsarin mulkin kasar mu. Dole DSS su bi ta kan Sowore domin ya na kiran juyin-juya-hali ne da nufin a kifar da zababbiyar gwamnati mai-ci.”

“Yayi wannan kira a talabijin, da kafar gidan jaridar sa ta yanar gizo wanda ta ke aiki daga kasar Amurka. Sowore ba gama-garin mutum ba ne wanda ke bayyana ra’ayinsa a kafafen sadarwa.”

“Ya yi takarar shugaban kasa – ya kuma sha kashi – a karkashin jam’iyyar AAC a zaben bana. Ba daidai ba ne Yele Sowore ya rika kira a kifar da farra hular da aka sha wahala kafin a kafa ta.”

KU KARANTA: Jami'an Hukumar DSS sun saki Omoyele Sowore

Shugaban Najeriyar ya nuna cewa Sowore ba kamar sauran ‘Yan gwargwarmaya ba ne domin ya na rajin ganin an kifar da gwamnatin farar hula bayan shekaru ana ta gwa-gwa-gwa da Soji.

Shehu ya ce: “Najeriya ba ta bukatar wani danyen aikin rashin bin doka da mutuwar al’umma da sunan juyin juya-hali, musamman ga mutumin da gidansa ya ke can nesa a Birnin New York.”

Fadar shugaban kasar ta cigaba da cewa: “Sowore ya na iya tserewa a ko yaushe bayan ya tada zaune-tsaye. Kamar dai Nnamdi Kanu.” "DSS ta yi aiki da karfin da doka ta ba ta." Inji Buhari.

Da farko jama'a sun fito su na zargin jami'an DSS da shiga cikin kotu domin su damke Yele Sowore. Daga baya hukumar ta fito ta yi bayani tsaf game da abin da ya wakana a wancan Ranar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel