Jami'an Kwastam sun damke mutum da shinkafa kanannade a jikinshi (Bidiyo)

Jami'an Kwastam sun damke mutum da shinkafa kanannade a jikinshi (Bidiyo)

Jami'an hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam sun damke wani matashi da ya kanannade shinkafa a jikinsa domin shigo da su Najeriya.

A bidiyon da muka samu a manhajar Facebook, an ga jami'in kwastam yana yanke selotep din da akayi amfani da shi wajen daure shinkafar a sassan jikinshi daban-daban. An daura wasu a kirginsa, wasu a kafansa.

Ana iya jin murya a cikin bidiyon inda jami'in ke cewa mai laifin dake kokarin boye fuskarsa ya daga kai ya fuskanci kamara.

Daga baya daya daga cikin jami'an ya kawo buhu domin juya shinkafar gwamnatin ciki.

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Mata 800,000 ke fama da ciwon yoyon fitsari a Najeriya - Majalisar dinkin duniya

Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabrin, Kanar Hamid Ali, ya ce rufe iyakokin Najeriya da akayi zai yi matukar taimakawa cigaban kasar.

Yace: "Wannan gwamnati ce wacce ta lashi takobin cewa wajibi ne mu gina Najeriya, mu ci kayan noman Najeriya."

"Kasar Sin da muke zuwa siyo kusan dukkan kayayyakin da muke amfani da su, shin kun san shekaru nawa suka rufe iyakokinsu? Sun rufe iyakokinsu na tsawon shekaru 40 kuma gashi yau sun girma. Shin baku son Najeriya ta girma ne?"

Hamid Ali ya yi watsi da maganar da mutane ke yi cewa rufe boda ya tsananta halin yunwa da kuncin da yan Najeriya ke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel