Aisha Buhari, Bindow, SGF, Minista sun gaza fitar da APC kunya a zaben kananan hukumomi a Adamawa

Aisha Buhari, Bindow, SGF, Minista sun gaza fitar da APC kunya a zaben kananan hukumomi a Adamawa

Duk da kasancewa APC ta kunshi manyan mutane daga jihar Adamawa irinsu; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; ministan birnin tarayya (FCT), Musa Bello, Malam Nuhu Ribadu da tsohon gwamnan jihar, Sanata Umaru Bindow Jibrilla, jam'iyyar ta gaza samun koda kujerar shugaban karamar hukuma daya.

Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta kunshi manyan mutane da suka hada da shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa maso gabas, Salihu Mustapha, tsohon gwamna Murtala Nyako, Buba Marwa, Sanata Binta Masi, Sanata Aishatu Binani, Sanata Silas Zwingina da sauransu.

Sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Adamawa da aka kammala tattara wa ya nuna cewa jam'iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomin jihar a yayin da aka barke da zanga-zanga a kan sakamakon zaben.

Tun kafin zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar, 7 ga watan Disamba, jam'iyyar APC, reshen arewa maso gabas, ta kafa kwamitin mutane 39 da zai jagoranci dora jam'iyyar a kan turbar lashe zaben kananan hukumomin jihar Adamawa.

Sai dai, ana ganin tamkar kwalliyar jam'iyyar bata biya kudin sabulu ba, saboda hatta shugabanni da jagororin APC ba a gansu ba yayin da ake gudanar da zaben.

Duk kokarin jin ta bakin wasu daga manyan 'ya'yan jam'iyyar APC ya ci tura, saboda sun ki bawa manema labarai fuskar yi musu tambayoyi a kan zaben.

DUBA WANNAN: Sunaye: Matar ministan APC da sauran mutane 8 da Buhari ya amince da su a matsayin manyan sakatarori

Da take mayar da martani a kan sakamakon zaben ta bakin mai bata shawara a kan harkokin jam'iyya, Barista Shagnah Pwamaddi, APC ta yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana shi a matsayin wasan yara da ko kusa bai yi kama da zaben da ya amsa sunansa ba.

Ya kara da cewa sakamakon ba shine zabin jama'a ba tare da bayyana cewa jam'iyyar PDP ta yi amfani da jami'an tsaro da 'yan ta'adda wajen tafka magudi ta hanyar korar wakilan jam'iyyu da 'yan sa ido.

Kazalika, ya yi zargin cewa a wasu wuraren da aka sanar da sakamakon zabensu, jama'a basu ka jami'an hukumar zabe ba, balle kayan aikin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel