Sarki Sanusi ya aike wa gwamnatin tarayya sako

Sarki Sanusi ya aike wa gwamnatin tarayya sako

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta dau matakan gaggawa don gujewa nitsewar kasar nan a shekaru 10 masu zuwa.

Yayi kira ga gwamnatin tarayya tare da gwamnatocin jihohi da su fifita zuba hannayen jari a bangarorin kiwon lafiya da ilimi, don gujewa nitsewar kasar nan cikin mummunan hali.

Sarkin ya sanar da hakan ne lokacin da ya yi wa wakilan habaka cibiyoyin lafiya jawabi, a yayin da ya karbesu a matsayin mai masaukin baki.

Ya ce, "A shekaru biyu da suka gabata, na karanta rahoto a Bloomberg na rahoton bankin duniya a kan Najeriya, wanda aka fitar a ranar Litinin. Bankin duniyan ya yi hasashen cewa, matukar kasar nan ta cigaba da tafiya kamar yadda take, akwai yuwuwar nan da shekaru 10 Najeriya ta zamo gidan kashi 25 na matalautan duniya."

DUBA WANNAN: Sunaye: Matar ministan APC da sauran mutane 9 da Buhari ya aimce da su a matsayin manyan sakatarori

Basaraken ya kara da bayyana cewa, idan ba a dau mataki ba wajen shawo kan matsalolin nan, yawan mutane matalauta na kasar nan zasu kai miliyan 30 nan da shekaru 10.

Ya jaddada cewa, talauci ba a auna shi da yawan kudi. Ana auna shi ne da yadda ake samun ingantaccen ilimi, cibiyar kiwon lafiya, yawan mutuwar jarirai da mata masu juna biyu tare da rashin isasshen abinci nagari.

"Babbar hanyar kawo karshen talauci shine, saka hannayen jari a cibiyoyin lafiya da ilimi. A don haka ne muke kira ga gwamnatin tarayya da ta cigaba da kara kasafi a bangarorin nan don habaka shi.

"Ina kira ga bangarorin da ba na gwamnati ba da kuma masu ruwa da tsaki don saka hannayen jari a wadannan bangarorin. Ta wannan hanyar ne kadai za a iya gujewa faruwar hakan," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel