Hadiman Wase da Omo-Agege sun koka game da kin biyan albashi a Majalisa

Hadiman Wase da Omo-Agege sun koka game da kin biyan albashi a Majalisa

Wasu ma’aikatan da ke aiki a karkashin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Ahmed Wase, sun ce an hana su wasu kudinsu.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Manema labarai, Hadiman wadannan shugabannin majalisar tarayya sun bayyana cewa majalisa ta ki biyansu wasu daga cikin hakkokinsu bayan an dauke su.

Rahotannin sun bayyana cewa masu aiki a karkashin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Takwaransa na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ba su gamu da irin wannan matsala ba.

Wadannan Bayin Allah da aka dauka aiki a cikin Watannin Yuni da Yuli sun samu albashin watanni biyu ne rak duk da sun shafe watanni shida su na aiki da shugabannin majalisar tarayyar.

A Ranar Juma'a, 6 ga Watan Disamban 2019, Akawun majalisa Mohammed Sani-Omolori, ya bada umarni a dakatar da biyan ma’aikata. Wannan ya sa Hadiman su ka fara kai kara wajen Iyayen gidansu.

Wasu daga cikin Hadiman da ke taimakawa Sanata Ovie Omo-Agege da Ahmed Wase sun tabbatarwa Manema labarai cewa albashin Watan Oktoba da Nuwamba kurum aka biya su har yau.

KU KARANTA: Majalisar Wakilai za ta yi yunkurin sauke Shugaban kasa - Pelosi

Hadiman ‘Yan majalisan kasar da su ke tsoron su fito su yi magana a gaban Duniya saboda gudun jefa kansu a cikin matsala, sun bayyana cewa ana zaben masu kafa ne a majalisar ana biyansu.

“Ba ni kadai ba ne cikin matsalar, akwai wasu. Ina cikin wadanda Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya fara nadawa a Masu taimaka masa. Amma har yanzu ba a biya mu ba.”

“Sai su zabi wasu, su biya su, su kyale wasu sai wani Watan. Jiya da aka biya ni albashi na; na watanni biyu kurum aka bani – Oktoba da Nuwamba, a maimakon watanni shida.” Inji Hadimin.

“Da na tambayi dalili, sai aka fada mani CAN ya bada umarni daga yanzu a rika biyan albashin Oktoba ne zuwa gaba. Na kuma san wasu a ofishin mataimakin shugaban majalisa da abin shafa.”

Rashin biyan albashin na iya jawo zanga-zanga. Wani jami’in majalisar ya ce ana biyan Hadiman ne daga ranar da aka ba su takardun aiki, ba wai lokacin da su ka fara aiki da Iyayen gidansu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel