Amaechi: Gwamnati ta roki ‘Yan Najeriya da ke ketare su guji abin kunya

Amaechi: Gwamnati ta roki ‘Yan Najeriya da ke ketare su guji abin kunya

Harin da aka nemi a kai wa Rotimi Amaechi kwanan nan a kasar Sifen ya sa gwamnatin Najeriya ta fito ta na tir. Hukumar ‘Yan Najeriyar da ke kasashen ketare ta fito ta yi jawabi.

Yayin da Abike Dabiri-Erewa wanda ita ce shugabar wannan hukumar ta mutanen Najeriya da ke kasashen waje ta bayyana cewa za akwai hukuncin da ke jiran masu irin wannan danyen aiki.

Mista Abike Dabiri-Erewa ta roki ‘Yan Najeriya da su zama masu halin kirki da mutunci a ko ina su ka samu kasu. Dabiri-Erewa ta kara da cewa yin akasin ya na rusa darajar kasar a idon Duniya.

Hukumar ‘Yan Najeriya da ke kasashen waje ta yi Allah-wadai ko ta ina da harin da aka kai wa Ministan sufuri, Rotimi Amechi, a Garin Madrid da ke kasar Sifen, lokacin da ya ke wani aiki.

KU KARANTA: IPOB ta yi magana bayan ta kai wa Ike Ekweremadu mugun hari a Jamus

A daidai lokacin da Jakadancin Najeriya da Jami’an ‘Yan Sandan kasar Sifen su ke kokarin bincike lamarin, mu na kira ga ‘Yan Najeriya su zama masu dabi’ar kirkir a duk inda su ke.

Domin kuwa abubuwa irin wannan su na bata mutuncin kasar mu. Maganar ta hannun Jami’an tsaron Sifen, kuma wadannan mutane su san akwai hukuncin yin wannan mumumman aiki.

Hukumar ta Najeriya ta nuna cewa ba tare da wata-wata ba, jami’an tsaro za su bi diddikin duk abin da ya auku, sannan su cafke wadanda su ka yi wannan abin kunya, domin a hukuntasu.

Rotimi Amaechi ya hadu da wasu Tsageru ne a babban Birnin Madrid a Ranar Juma’a lokacin da ya ke halartar wani taro na Duniya. An yi dace jami’an tsaron kasar wajen sun tsare Ministan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel