'Yan fashi a cikin basaja sun kashe dan kasuwar canji a Abuja, sun gudu da buhun kudi

'Yan fashi a cikin basaja sun kashe dan kasuwar canji a Abuja, sun gudu da buhun kudi

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu 'yan fashi suka kai hari kasuwar 'yan canjin kudi da ke unguwar Zone 4 a babban birnin tarayya, Abuja, inda suka kashe wani dan kasuwa mai suna Alhaji Hamisu Naira.

A cewar rahotanni, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Alhamis, yayin da 'yan kasuwar canjin ke fito wa domin fara hada-hadar kasuwancin ranar.

Majiyar mu ta bayyana cewa 'yan fashin, wadanda suka yi basaja cikin shigar abokan kasuwanci, sun yi awon gaba da makudan kudin da ba a san adadinsu ba bayan sun kashe Alhaji Naira.

"Sun zo ne cikin shiga irin ta abokan kasuwanci, ba za a yi tunanin cewa 'yan fashi bane. Sun kira Alhaji Hamisu, bayan ya je sai kawai suka cakumi jakarsa wacce ke cike da kudaden gida da kasashen waje.

"Duk da hakan Alhaji Hamisu bai bari sun fizge jakar kudinnan daga hannunsa ba, saboda ba iya kudinsa bane kadai a cikinta. Ganin ya ki sakin jakar kudin ne sai mutanen suka fitar da bindiga suka harbe shi, sai a daidai lokacin ne hankalin yawancin jama'a ya kai ga abinda ke faruwa.

DUBA WANNAN: Dan sanda ya harbe wani matashi da ya rama marin da ya sharara masa

"Kafin jama'a su gama dawowa hayyacinsu daga firgitar jin tashin harbin bindiga, tuni 'yan fashin sun dauke jakar kudin sun figa da gudu a cikin motar da suka zo," kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana.

Wani shaidar ya kara da bayyana cewa sun iske gawar Alhaji Naira cikin jini, kuma sune suka sanar da ofishin 'yan sanda bayan sun gaggauta janye gawar marigayin.

Tuni an binne gawar Alhaji Naira, dan asalin karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa, bisa tsarin addinin Islama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel