Hukumar DSS ta wanke kanta, ta fadi masu hannu a cikin kokawar kama Sowore a cikin kotu

Hukumar DSS ta wanke kanta, ta fadi masu hannu a cikin kokawar kama Sowore a cikin kotu

Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya, DSS, ta tsame jami’anta daga kamen wasan kwaikwayon da aka yi yunkuri yi wa mawallafin Sahara Reporters kuma shugaban juyin juya hali na #RevolutinoNow, Omoyele Sowore, a cikin kotu.

Hukumar ta ce, magoya bayan Sowore ne suka tada hargitsi da rudani a cikin dakin kotun ba jami’anta ba.

A takardar da mai magana da yawun hukumar, Dr Peter Afunanya ya fitar, ya ce hukumar mai tsananin bin doka ce, a don haka ne ba zata taba yunkuirn kama Sowore a cikin kotu ba.

Afunanya ya kara da cewa, ko Lauyan Sowore, Femi Falana, ya tabbatar da cewa a wajen kotun ne hukumarsu ta kama wanda yake karewan.

DUBA WANNAN: Sunaye: Matar ministan APC da sauran mutane 9 da Buhari ya aimce da su a matsayin manyan sakatarori

“Akwai matukar amfani idan hukumar jami’an tsaro ta farin kaya ta yi cikakken bayani game da labaran da ake yadawa a kafafen yada labarai. Babu sa hannunta a lamarin da ya faru a dakin kotun tarayya da ke Abuja a ranar 6 ga watan Disamba. Tun farko, Lauyan Sowore ya jawo hankalin alkalin a kan cewa, hukumar na shirya kara kama wanda yake karewa idan an kammala zaman kotun,

“Kotun ta yi watsi da wannan koken nashi tare da tabbatar mishi cewa hukumar na bin doka ne kuma ba zata kwatanta yin hakan ba. Daga nan sai aka dage sauraron shari’ar zuwa watan Fabrairu na 2020.

“Amma kuma, lokacin da Sowore ya fito daga kotun sai ya ci karo da jami’an hukumar, hakan yasa ya ruga tare da shigewa dakin kotun. A kokarin kangeshi daga wannan hasashen kamen, magoya bayanshi sun kada shi kasa tare da ihun cewa “ba zaku kama shi ba”. Lamarin da ya jawo wannan rudanin.” in ji takardar

“Idan mutum ya kalla wanna bidiyon da ke yawo da kyau, zai ga babu jami’in DSS ko daya a ciki, yayin da wannan wasan kwaikwayon ya auku a cikin kotu. Ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa, kotun ta dage sauraron shari’ar cikin lumana amma kwatsam sai wannan rudanin ya barke. An kara kama Sowore ne a wajen kotun ba cikinta ba." Takardar ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel