Dan sanda ya kashe wani matashi da ya sharara masa mari

Dan sanda ya kashe wani matashi da ya sharara masa mari

Wani dan sanda ya harbe wani matashi, mai shekaru goma sha takwas, da ya rama marin da jami'in ya yi masa.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba, a harabar reshen wani banki da ke Umuaka a jihar Imo.

A cewar rahotanni, matashin, Awuzie Duru, ya je harabar bankin ne domin ya fitar da kudi daga na'aurar ATM, kuma ya hau layi, kamar yadda ya zo ya tarar, bisa tsari.

Bayan wani dan lokaci, sai Awuzie ya bar layi domin ya amsa waya, amma da ya dawo sai wanda yake bayansa ya ki matsa masa wuri domin ya koma layi. Hakan ne kuma ya haddasa cacar baki a tsakanin matashin da mutumin.

Nan da fada ya kaure a tsakaninsu, lamarin da ta kai ga dan sandan da ke bakin shiga bankin ya zo domin shiga tsakaninsu.

A cewar shaidar gani da ido, dan sandan ya rufe Awuzie da fada bayan zuwansa, shi kuma cikin fushi ya fada wa dan sandan cewa bai kawo agaji domin kwatar masa hakkinsa, a saboda haka bai kamata yake zaginsa ba.

A daidai wannan lokacin ne aka ce dan sandan ya sharara wa Awuzie mari saboda ya tanka masa. Bayan Awuzie ya rama marin ne sai jami'in dan sandan ya fitar da bindigarsa ya harbe matashin, wanda nan take ya fadi matacce, kamar yadda shaidun suka sanar.

Batun kisan matashin ta haddasa barkewar kwarya-kwaryar rikicin da har ta kai ga wasu fusatattun matasa sun fara tsara yadda zasu kai wa ofishin 'yan sandan yankin harin daukan fansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel