Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Reinhard Bonnke

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Reinhard Bonnke

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta mutuwar Reinhard Bonnke, da babban rashi a duniya

- Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin kasar Jamus, jama'ar kasar da kuma duk fadin duniya

- Ya kara da yi wa babban malamin addu'ar rahama tare da fatan iyalansa zasu jure wannan babban rashin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta mutuwar Reinhard Bonnke, wani malamin addinin kirista dan asalin kasar Jamus, da babban rashi ga Najeriya.

Bonke ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekaru 79 a duniya.

A wata takarda, Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin kasar Jamus da kuma iyalan mamacin. A yayin ta'aziyya ga wadanda rashin ya shafa, shugaban kasar yace babban malamin ya kawo sakon Yesu har nahiyar Afirka.

DUBA WANNAN: Amosun da wasu mutane 3,000 sun dunguma sun koma jam'iyyar PDP

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi ayarin mabiya addinin kirista wajen makokin mutuwar sanannen malamin Reinhard Bonnke, mai shekaru 79 a duniya. Wannan babban rashi ne ga Najeriya, Afirka da duniya baki daya,” in ji takardar.

Shugaban kasar ya jajantawa jama’ar kasar Jamus tare da gwamnatin, iyalansa, abokan yada addinin da kuma masu koyar da littafi mai tsarki. Ya yi addu’ar Ubangiji ya basu hakurin jure wannan rashin.

Shugaba Buhari ya kara da bayyana cewa, jihadin Bonnke a Najeriya, Afirka da duniya sun isar da sakonnin Yesu. Ya kara da addu’ar rahama da jin kai ga malamin. Ya kara da tabbatar da cewa, Ubangiji zai rahamsheshi sakamakon gudummawar da ya bawa addini a fadin duniya," in ji takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel