Aisha Buhari ta yi wa minister kaca-kaca, ta bukaci a rika hukunta masu zagin shugaban kasa

Aisha Buhari ta yi wa minister kaca-kaca, ta bukaci a rika hukunta masu zagin shugaban kasa

Matar Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha ta zargi hadiman mijinta da ministan sadarwar, Isa Ibrahim da rashin daukan matakan da suka dace domin hukunta wadanda ke yadda labaran karya musamman kan mijinta kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Aisha Buhari ta ce wasu 'yan Najeriya suna kokarin amfani da kafafen sada zumunta domin 'hargitsa gwamnati' yayin da jami'an gwamnatin ba su daukan wani matkin da ya dace a kan masu yada labaran karya wadda hakan na bawa mutane damar cin mutuncin Buhari ta tare da an dauki mataki a kansu ba.

"Kamata ya yi ministan sadarwar ya bayar da umurnin a kawo karshe yadda labarun karya, ba wai ayi magana a kansa ba kowa ya yi dariya shi kenan. Babu wani hukunci kan wadanda suka aikata laifin, hakan na nufin kowa zai iya aikata abinda ya ke so ba tare da hukunci ta hau kansa ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar Ganduje zai nada Sarkin Bichi shugaban sarakunan Kano

"Babu yadda za ayi a samu zaman lafiya a irin wannan yanayi. Idan babu hukunci, kowa zai rika aikata duk abinda ya ga dama ne kuma kusan komai zai rikice," inji Aisha Buhari.

Uwargidan shugaba Buhari, babbar mai goyon bayan wannan dokar ce ta tsarkake kafafen sada zumunta ne kasar na. Ta bayyana matsayarta ne a wata tattaunawar waya da aka yi da ita a shirin ‘Journalists’ Hangout’ na gidan talabijin na TVC a ranar Juma’a da yamma.

Ta ce, hadimin ya kasa kare mutuncin Buharin amma ya iya hanzari wajen shawo kan matsalolin da basu da muhimmanci.

“A lokacin da yakamata a dau mataki a kan masu laifi, ko kuma a ja kunnen mutane, sai su yi mukus,” in ji ta.

"Amma idan abubuwan da ba su da muhimmanci ne mutane za su fara magana kan shugaban kasa. Misali shine abinda ya faru bayan zaben Bayelsa. Lokacin da PDP ta fito ta ce za ta dakatar da tsohon shugaba, Goodluck Jonathan kan aikata wani laifi ko wani abu mai kama da haka.

"Ban ga dalilin da zai sa fadar shugaban kasa ta fito ta ce tayi mamakin jin hakan ba. Matsalar su ne? Su 'yan PDP ne? Shin Jonathan dan jam'iyyar mu ne? Mene hadin fadar shugaban da lamarin?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel