Sunaye: Matar ministan APC da sauran mutane 9 da Buhari ya aimce da su a matsayin manyan sakatarori

Sunaye: Matar ministan APC da sauran mutane 9 da Buhari ya aimce da su a matsayin manyan sakatarori

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada Dakta Evelyn Ngige, matar ministan kwadago da aiyuka, Dakta Chris Ngige, da sauran wasu mutane takwas a matsayin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya.

Mukaddashin shugabar hukumar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan, ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da darektan yada labarai a ofishinta, Olawunmi Ogunmosunle, ta fitar a Abuja.

A cewar ta, jerin sunaye da jihohin haihuwar mutanen da aka nada a matsayin manyan sakatarorin sune kamar haka, Injiniya Musa Hassan daga jihar Borno; Mista Ahmed Aliyu daga jihar Neja; da uwargida Olushola Idowu daga jihar Ogun.

DUBA WANNAN: Bincike: Yadda Yari ya biya kansa miliyan N522 ana saura kwana 2 ya mika mulki

Ragowar mutane shidda da aka nada bisa shiyya shidda na kasa sune kamar haka; Andrew David Adejoh daga arewa ta tsakiya; Umar Tijjani daga arewa ta gabas; Dakta Nasir Sani Gwarzo daga arewa maso yamma; Injiniya Nebeolisa Victor Anako daga kudu maso gabas; da Temitope Peter daga kudu maso yamma.

Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da ranar da za a rantsar da sabbin sakatarorin da kuma sanar da ma'aikatun da zasu jagoranta nan bada dade wa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel