2020: NAHCON ta bayyana adadin kejerun aiki Hajji da Saudiyya za ta bawa Najeriya

2020: NAHCON ta bayyana adadin kejerun aiki Hajji da Saudiyya za ta bawa Najeriya

Hukumar kula da aiyukan Hajji taa Najeriya, NAHCON, a ranar Asabar tace ta samu kujeru 95,000 na maniyyatan aikin Hajji na shekarar 2020.

Wannan na kunshe ne a takardar da shugabar bangaren hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta ba manema labarai a garin Abuja.

Ta ce, an sa hannu a yarjejeniya tsakanin karamin ministan harkokin waje na Najeriya, Zubairu Dada da kuma ministan aiyukan Hajji da Umara, Saleh Benten.

Ta ce, an sa hannu a kan yarjejeniyar ne a ranar 5 ga watan Disamba, a shirye-shiryen aikin Hajji na 2020.

“A yayin saka hannun, Ambasada Dada ya mika godiyar Muhammadu Buhari ga Sarki Salman Bin Abdulaziz da kuma hukumomin aiyukan Hajji da suka biya diyyar mutane biyar da suka rasu tare da mutane shida daga Najeriya da suka yi hatsari a Makkah,” in ji ta.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Manyan jarumai 5 mata na Kannywood da su kayi tashe a baya

Kamar yadda ministar ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika godiyarsa a kan karamci da goyon baya da mahajjatan Najeriya ke mora a kasar ta Saudi Arabia.

Dada ya ce, shugaba Buhari ya kara da mika kokon barar bukatarsa ga hukumomin Saudi Arabia da su cigaba da bada taimako ga NAHCON ta kowacce siga da ta shafi mahajjatan kasar nan.

Abdullahi Saleh, mukaddashin shugaban NAHCON kuma mukaddashin kwamishinan aiyuka na hukumar, ya bayyana godiyarsa ga ma’aikatar aiyukan Hajji da Umarah. Ya kara da kira garesu a kan hadin kansu da goyon bayansu a kowanne bangare.

Kamar yadda yarjejeniyar ta bayyana, “mahajjata zasu iya biyan riyal 100 ko sama da haka don ta zame musu inshorar hadurra, asarar dukiya da sauran hadurra da mahajjata kan iya fuskanta. Amma kuma hakan bai shafe kudin magani ba a kasar ta Saudi Arabia.”

“A bayani a kan hatimin shiga kasar, wakilan sun yanke riyal 300 na kowanne irin hatimi,” takardar ta ce.

Takardar ta kara da cewa, hatimin bai shafe daga lokacin Umara ko ziyara ba zuwa lokacin Hajji.

Jakadan kasar Saudi Arabia din ya kara da jinjinawa kokarin NAHCON wajen hana take sharuddan hatimin shiga kasar tare da al’amuran da suka shafi aikin hajji. Ya tabbatarwa da NAHCOn cewa, Saudi Arabia zata kara gina makewayi 60,000 don shawo kan matsalolin makewayi da ake fuskanta a yayin aikin Hajjin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel