Bincike: Yadda Yari ya biya kansa miliyan N522 ana saura kwana 2 ya mika mulki

Bincike: Yadda Yari ya biya kansa miliyan N522 ana saura kwana 2 ya mika mulki

- Bincike ya bankado yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya biya kansa da mataimakinsa makudan miliyoyi kafin su bar gwamnati

- Rohoton bincike ya gano cewar tsohon gwamnan ya fitar da kudin yawansu ya kai miliyan N525 ana saura kwana biyu ya bar ofis

- Jaridar Premium Times ta bayyana cewa Yari ya biya kansa miliyan N350 daga cikin kudaden

Wani rahoton bincike da jaridar Premium Times ta gabatar ya bankado yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya biya kansa da mataimakinsa jimillar kudin da yawansu ya kai miliyan N525 ana saura kwana biyu su bar Ofis.

A cewar rahoton binciken da jaridar ta gudanar, Yari ya biya kansa miliyan N350 daga cikin adadin kudin.

An biya tsohon gwamnan da mataimakinsa kudin ne daga asusun 'yan fansho a reshen daya daga cikin bankunan kasar nan da ke Gusau a ranar 27 ga watan Mayu, 2019.

Kazalika, an biya tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakala, miliyan N175 daga cikin adadin kudin.

Takardun sun nuna cewa an biya Yari kudin ne a matsayin rance domin sayen wani gidan alfarma a unguwar Maitama bisa tsarin dokar 'yan fansho.

DUBA WANNAN: Dalilina na zaben 'yan APC a cikin sabbin kwamishinoni - gwamna Matawalle

Sai dai, sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya soke wannan doka tare da bayyana cewa, "babu yadda za a yi jihar Zamfara ta cigaba da biyan tsofin shugabanni irin wadannan makudan kudi duk shekara a yayin da sauran 'yan jiha ke cikin tsanani.

Yari ya rubuta wa gwamnan Matawalle takardar neman karin biyansa miliyan N10 duk wata bayan miliyan N702 da doka ta amince za a ke biyansa da mataimakinsa duk shekara.

Batun alawus da fanshon ysofin gwamnoni ya dade da zama darasin tattauna wa a tsakanin 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel