Sowere: NBA ta bukaci FG ta gaggauta dakatar da darektan DSS

Sowere: NBA ta bukaci FG ta gaggauta dakatar da darektan DSS

Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta dakatar da babban darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yuusf Magaji Bichi.

NBA ta yi wannan kira ne a matsayin martani ga sake kama Omoyele Sowore da jami'an hukumar DSS suka yi bayan kotu ta bayar da umarnin a sake shi.

Jami'an hukumar DSS sun dira a kotu tare da sake kama Sowore kasa da sa'o'i 24 bayan sun sake shi bisa umarnin kotu.

A jawabin da NBA ta fitar ta bakin Kunle Edun, sakataren yada labarai, kungiyar ta ce hukumar DSS ta zama marar da'a da girmama umarnin kotu a karkashin jagorancin Bichi.

Bayan ta yi watsi tare da Alla wadai da abinda hukumar DSS ta aikata, NBA ta gabatar da jerin wasu bukatu guda 4 kamar haka:

DUBA WANNAN: Mun bankado yunkurin hargitsa Najeriya - DSS

1. Gwamnatin tarayya da majalisa su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wani mai hannu a cikin abinda ya faru.

2. FG gaggauta dakatar da darektan hukumar DSS saboda rashin girmama umarnin kotu da girmama hakkin 'yan kasa da DSS ke yi a karkashin jagorancinsa.

3. Majalisa ta sake duban dokokin kundin hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa sun yi daidai da tsarin dimokradiyya.

4. Muna kira ga ministan shari'a na kasa da ya karbi ragamar duk wata Shari'a da ta shafi siyasa daga hannun hukumomin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel