Bamu kama shi ba wannan karon, amma tabbas sai munyi mishi dukan tsiya idan muka kama shi - Cewar wadanda suka kaiwa Amaechi hari

Bamu kama shi ba wannan karon, amma tabbas sai munyi mishi dukan tsiya idan muka kama shi - Cewar wadanda suka kaiwa Amaechi hari

- ‘Yan kungiyar IPOB sun tabbatar da harin da suka kaiwa ministan sufurin Naeriya kuma tsohon gwamnan jihar Ribas

- Sun nuna matukar damuwarsu da bakin cikinsu na rashin samun ministan, amma sun sha alwashin zai sha jibga

- A bidiyon da suka wallafa na wajen da abun ya faru, an ji suna mishi ihu tare da kiranshi da dan ta’adda kuma barawo

‘Yan kungiyar IPOB sun tabbatar da harin da aka kaiwa ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi a kasar Spain.

LIB ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Rivers din ya bayyana yadda aka hareshi a Spain. Ya kwatanta wadanda suka hareshin da ‘wasu karkatattun ‘yan Najeriya’. Sun kuma hare shi din ne bayan da ya je wani aikin kasa a Turai din.

“Mintoci kadan da suka gabata, wasu karkatattun ‘yan Najeriya sun hareni a lokacin da aka aika ni don aikin kasata a Madrid, Spain,” ministan ya wallafa a shafinsa na tuwita a ranar Juma’a.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, wasu ‘yan kungiyar IPOB din sun wallafa bidiyo a inda abun ya faru. Suna matukar nuna bakin cikinsu na ‘rashin samun ministan’. Sun kara da cewa, babu shakka zasu ‘kamashi kuma su jibgeshi’.

KU KARANTA: Innalillahi: Saurayi ya kashe budurwa ya yanke mata kai ya ciro kwakwalwarta ya dafa ya cinye kamar abinci

A bidiyon da suka wallafa, anji ‘yan kungiyar na ihu da sowa kuma suna cewa, “Dan ta’adda ne, barawo ne”.

Ba dai yanzu ne ‘yan kungiyar IPOB din suka fara harar jiga-jigan siyasar kudancin kasar nan ba a kasashen ketare. Idan ba zamu manta ba, jigo Eke ya sha mugun duka kwanakin baya a kasar ketare.

Hakazalika, sun sha alwashin cin zarafin duk wani gwamnan da baya biyan albashi, matukar suka ci karo da shi a kasar ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel