Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar Ganduje zai nada Sarkin Bichi shugaban sarakunan Kano

Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar Ganduje zai nada Sarkin Bichi shugaban sarakunan Kano

Alamu sun nuna cewa, Gwamna Abdllahi Umar Ganduje na jihar Kano zai nada Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban kungiyar sarakunan jihar Kano kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Bayan da gwamnan ya bayyana hikima da basirar da ke kunshe da samar da karin masarautun hudu a jihar, Ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba zai bayyana shugaban kungiyar sarakunan jihar.

Kamar yadda wata takardar da Malam Abba Anwar,babban sakataren yada labarai na gwamnan ya sa hannu, ya bayyan cewa, gwamnan ya bada wannan sanarwan ne a hirar da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels mai taken ‘Halin da kasar nan ke ciki’, a ranar Juma’a tsakanin 7:30 zuwa 8:00 na dare.

Kamar yadda takardar ta sanar, Ganduje ya tabbatar da cewa, sabbin sarakunan Bichi, Karaye, Rano da Gaya an kawosu ne don cigaba da habaka jihar Kano din.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Ya ce, dokar ta ba gwamnan damar zaben wanda zai shugabanci majalisar sarakunan jihar don juya lamurran sarakunan biyar na jihar.

A yayin bayani a kan yadda aka kirkiro masarautun, gwamnan ya ce, “Hikimar kirkirar karin masarautun hudu tuntuni na bayyana su. Daga cikin dalilan, mutanen jihar ne suka bukaci hakan saboda sun damu da samun cigaba da habakar jihar da mutanen jihar".

“An samu irin wannan bukatar a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abubakar Rimi. Amma a wancan lokacin, ba a bi dokokin da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar na kirkirar sabbin masarautun ba. Wannan ne ya zamo hanya mafi sauki da gwamnatin da ta gajeshi ta warware masarautun.” takardar ta ce.

“Amma bayan yin biyayya ga dokar kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999, kamar yadda aka gyara, sabbin masarautun sun kafu kuma zasu zauna daram ko bayan nan.” In ji shi.

Ya tabbatar da cewa, an bi duk tanadin shari’a wajen kirkirar masarautun kuma suna nan daram ba gudu ba ja da baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel