An harbe wasu samari guda 4 da aka kama sun yiwa budurwa fyade sun kuma kasheta

An harbe wasu samari guda 4 da aka kama sun yiwa budurwa fyade sun kuma kasheta

- ‘Yan sandan kasar Indiya sun harbe wasu samari 4 da aka kama da laifin yi wa wata likitar dabbobi fyade tare da kasheta

- Sun sace mata tayar mota sannan suka jira ko zata nemi taimako. Bayan ta nemi su taimaka mata ne suka yi amfani da damar don cutarta

- Tuni dai kasar Indiya ta cika da murna, biki, bidiri da shagali a kan hukuncin da aka yankewa miyagun mutanen

Hukumar ‘yan sandan kasar Indiya sun harbe wasu maza hudu da aka kama da laifin yi wa wata likitan dabbobi fyade kuma suka kone gawarta kurmus.

Labarin kisan masu laifin ya fantsama a kasar Indiya kuma ya jawo murna da jin dadi ga mutane. Hatta mahaifiyar daya daga cikin samarin da aka kashe, cewa ta yi “An yi adalci”.

Kamar yadda rahoton BBC ya nuna, mazauna yankin sun yi biki, bidiri tare da murnar kisan samarin. Taron mutane masu yawa ne suka taru a inda aka kashesu suna jinjinawa ‘yan sandan. Wasu kuwa har da alawa suka dinga ba jami’an ‘yan sandan don nuna farincikinsu su tare da girmamawa ga ‘yan sandan.

“Ban san yadda zan kwatanta ba, amma ina matukar farin ciki kuma da bakin ciki a lokaci guda. Saboda ‘ya ta ba zata taba dawowa gida ba. Ban taba tsammanin za a yi mana adalci ba. Bana fatan abinda ya faru da ‘ya ta ya faru da wata,” mahaifiyar wacce aka yi wa fyaden ta bayyana.

Ta kara da cewa, akwai bukatar a kara tsaurin hukuncin ga masu cin zarafin ‘ya’ya mata.

KU KARANTA: Tirkashi: Daga kai 'yarta Fasto ya cire mata aljanu, sai ta kama shi yana lalata da ita

“Kamata ya yi maza su dinga jin tsoron kallon mata, saboda irin hukuncin da zasu fuskanta,” in ji ta.

Priyanka Reddy likitan dabbobi ce mai shekaru 27 a duniya. Tayarta ta sace ne inda mazan suka nemi da su taimaka mata. Amma daga baya sai suka kare da yi mata fyade tare da kasheta har lahira.

Kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta sanar, an gano cewa samarin ne suka sace mata tayar, sannan suka jira ko zata nemi taimako. Sun kara da bayyana cewa, sun yi mata fyade kuma sun shaketa har sai da ta mutu.

Samarin sune: Mohammed Areef mai shekaru 26, direban babbar mota ne, Jollu Shiva mai shekaru 29 kuma mai goge-goge ne. Jollu Naveen mai shekaru 20 direba ne, sai Chintakunta Chennakeshavulu mai shekaru 20 asalin dan Gudigandia ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel