NBS: Kiyasin ma'aikatu da suka fi cin rashawa a Najeriya

NBS: Kiyasin ma'aikatu da suka fi cin rashawa a Najeriya

Jami’an hukumar ‘yan sandan Najeriya sun cigaba da tsare matakinsu na kan gaba a kan hukumar da rashawa ta yi mata katutu a Najeriya, kamar yadda rahoton hukumar kiyasi ta kasa ya bayyana.

Rahoton mai taken, ‘Kiyasin rashawa kashi na biyu a Najeriya’, an sake shi a ranar Juma’a a garin Abuja.

Hukumar kiyasin ta Najeriya ta yi kiyasin ne tare da hadin guiwar ofishin majalisar dinkin duniya a kan miyagun kwayoyi da sauran manyan laifuka.

An mika abinda rahoton ya gano ne a taron da aka yi a dakin taro na gidan gwamnati a Abuja. Shugaban hukumar NBS din, Dr Yemi Kale ne ya gabatar da kiyasin a taron.

An fara bayyana kiyasin rashawa na farko a Najeriya ne a 2016, inda hukumar ‘yan sanda a Najeriya ce ta fi kowacce cibiya a kasar cin rashawa.

DUBA WANNAN: Ina bukatar a damko wadanda suka kai min hari a majalisar dattijai - Hadiza Bala Usman

A rahoton 2019, bayan shekaru uku da tsohon rahoton, ‘yan sandan ne suka samu darewa a lamba ta daya. Kiyasin na nuna cewa, kashi 3 na jami’an hukumar ne ke cin rashawa. An kuwa samu cigaba don kuwa a 2016 kashi 46 ne ya nuna.

Wadanda ke biye da ‘yan sandan sune hukumar rijistar filaye masu kashi 26, sai jami’an hukumar kudin shiga wadanda ke da kashi 25. Na kasa a kiyasin sune ma’aikatan lafiya masu kashi 5 kacal.

Hukumar NBS ta kwatanta rahoton 2019 din da ‘matsalar da aka raina a cikin gida’, ta ce ta tattara bayanai ne daga mutane 33,067 a jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayyar Najeriya ta hanyar tattaunawa.

Rahoton ya bada kiyasin jihohi daya bayan daya, inda jihar Kogi ta zamo kan gaba da kashi 48, jihar Gombe ke biye da kashi 45, jihar Rivers ta samu kashi 43 sai kuma jihar Adamawa da ta samu kashi 41.

Jihar Imo ce ta zo karshe a kiyasin da kashi 17.6, jihohin Jigawa, Kano da Filato ke biye da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel