2023: Wata kungiyar Arewa ta mara wa Tinubu baya

2023: Wata kungiyar Arewa ta mara wa Tinubu baya

Wata kungiyar matasa a arewa ta goyi bayan a mayar da mulki zuwa kudancin Najeriya bayan karewar wa'adin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kungiyar, Tinubu North West Ambassador, ta ce ya kamata a zabo shugaban kasa daga kudancin Najeriya saboda hadin kai, zaman lafiya da kara dankon zumunci tsakanin 'yan kasar.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhassan Muhammad wanda ya zanta da manema labarai bayan tattakin da su kayi na yankin Arewa maso yamma, ya ce sunyi tattakin ne domin neman goyon bayan al'umma kan bukatarsu na mayar da mulki zuwa kudu.

Ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan kiraye-kirayen da wasu fitattun shugabanin arewa keyi na neman yankin ta cigaba da mulkar kasar a 2023 inda ya yi kira ga 'yan Najeriya kada su goyi bayan su.

DUBA WANNAN: Miyagu sun karbe kasa daga hannun Buhari - Aisha Buhari

Alhassan ya ce, "Abinda ya dace shine shugabanin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki suyi aiki tare da bayar da goyon bayansu domin ganin dukkanin manyan jami'iyyun siyasa sun tsayar da 'yan takara daga kudancin Najeriya.

"Muna neman a tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya da ke da akida irin ta Buhari kuma wanda ke da kwarewa da zai iya mulkar Najeriya.

"Mu a matsayin mu na kungiya mun yanke shawarar goyon bayan tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu."

Kungiyar ta kara da cewa, "Tinubu yana daya daga cikin masu 'son cigaba' da ya nuna kwazo da sadaukar da kai don neman cigaban Najeriya.

"Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin cigaban jam'iyyar APC da Shugba Muhammadu Buhari a zabukkan 2015 da 2019 saboda ya yi imani da tsare-tsaren da APC ke da niyyar aiwatar wa a Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel