Amosun da wasu mutane 3,000 sun koma PDP a jihar Ogun

Amosun da wasu mutane 3,000 sun koma PDP a jihar Ogun

'Yan jam'iyyar Alliance for New Nigeria (ANN) fiye da 3,000 ne suka dunguma suka koma jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) gabanin zabukan kananan hukumomi da za a gudanar a jihar ta Ogun a sabuwar shekarar da za a shiga kafin daga bisani a yi babban zabe a 2023.

Masu sauya shekar da dan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar ANN mai wakiltan Abeokuta ta Kudu, Akeem Amosun ya jagoranta sun ce sun koma jam'iyyar ta PDP ne domin su hada karfe da karfe wuri guda su kafa jam'iyyar adawa mai karfe a jihar.

Dan majalisa, Hon. Ladi Adebutu da jigo a jam'iyyar PDP, Sikurullai Ogundele ne suka karbi tsaffin 'yan jam'iyyar ta ANN da suka shigo PDP a ranar Alhamis.

Akeem Amosun ya shaidawa manema labarai cewa sun yanke shawarar komawa PDP ne domin hakan zai taimake shi cimma burinsa na siyasa.

DUBA WANNAN: Miyagu sun karbe kasa daga hannun mu - Aisha Buhari

Adebutu ya yi maraba da sabbin 'yan jam'iyyar inda ya ce ya zama dole su hada hannu wuri guda duba da cewa a halin yanzu zabukkan kasar nan sun zama harka da ake amfani da jami'an tsaro.

Ya ce: "Abokan hammayar mu ba su da tausayi, dole mu hada kai wuri guda. Ina kira ga dukkan jam'iyyu su hada kai su zama tsintsiya madaurin ki daya saboda idan sun zo da 'yan dabarsu daga Legas za mu iya kare kanmu.

"Gwamnatin APC a jihar mu ba ta iya tabuka komi kuma ba ta da tausayi. Ba su iya aikata komi sai sun samu izini daga Legas. Jihar Ogun ba karkashin Legas ta ke ba.

"Abinda muka saka a gaba shine yadda za mu ceto jihar mu daga hannun wadanda ba su da tausayi kuma ba su san aiki ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel