Hukumar Mayakan sama ta yaye jami'ai 717 da aka horar kan dakile yan baranda (Hotuna)

Hukumar Mayakan sama ta yaye jami'ai 717 da aka horar kan dakile yan baranda (Hotuna)

Hukumar Sojin saman Najeriya ta sake yaye jami'ai 717 da aka horar kan dakile rikice-rikicen cikin gida da suka addabi sassan kasa na masu garkuwa da mutane da yan aware.

An gudanar da taron yaye daliban ne a dakin taon Shittu Alao dake gidan horon Soji RTC, jihar Kaduna a ranar Juma'a, 6 ga watan Disamba, 2019.

Kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu, an horar da jami'ai 3,629.

Masu horon sun hada da manyan Sojojin Najeriya da na kasashen waje.

A jawabin da ya saki yace: "Babban hafsan hukumar mayakan sama, AM Sadique Abubakar ya bayyana cewa gidan horon Soji RTC ta cigaba da kasancewa gidan ilmantar da Soji wajen yaki da kare dukiyoyin kasa."

"Ya bayyana cewa irin horon da ake bayarwa a RTC ya nuna irin namijin kokarin da jami'an da aka tura atisaye wurare 10 a fadin tarayya suke yi wajen dakile barandanci, ta'addanci da sauransu."

"Air Marshal Abubakar ya yi alkawarin cewa hukumar za ta cigaba da ilmantar da jami'ai domin dakile rashin tsaron kasa."

Hukumar Mayakan sama ta yaye jami'ai 717 da aka horar kan dakile yan baranda (Hotuna)

Hukumar Mayakan sama ta yaye jami'ai 717
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel