An tura sabon kwamishinan Yansanda a jahar Adamawa saboda zaben kananan hukumomi

An tura sabon kwamishinan Yansanda a jahar Adamawa saboda zaben kananan hukumomi

Yayin da ake tsumayin zaben kananan hukumomin jahar Adamawa, babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohamemd Aubakar ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar domin sanya idanu a zaben tare da tabbatar da zaman lafiya a yayin zaben.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito sabon kwamishinan da aka tura jahar Adamawa sunan sa Philip Maku, kuma kwamishinan ya tabbatar ma al’ummar jahar cewa rundunar Yansanda za ta tabbatar da tsaro a jahar a yayin zaben na ranar Asabar, 7 ga watan Disamba.

KU KARANTA: An yi asarar rai a wani rikici tsakanin Fulani da Hausawa a Jigawa

An tura sabon kwamishinan Yansanda a jahar Adamawa saboda zaben kananan hukumomi

Philip Maku
Source: Facebook

“An turo ni jahar Adamawa ne domin na sa ido a zaben kananan hukumomin jahar wanda za’a gudanar a ranar Asabar, 7 ga watan Disamba, ina tabbatar ma jama’a cewa za’a baza jami’an tsaro daga sauran hukumomin tsaro a dukkanin rumfunan zabe domin tabbatar da jama’a sun kada kuri’unsu ba tare da tsoro ko cin zarafinsu ba.

“Ina kara yin gargadi ga masu shirin yin magudin zabe, domin kuwa ba zamu lamunci duk wasu na’u’in satar kuri’u, magudin zabe da rikice rikicen siyasa ba, haka zalika zamu gudanar da binciken ababen hawa a ranar zabe, kuma a shirye muke mu kama duk wasu masu tayar da zauni tsaye a jahar.” Inji shi.

Bugu da kari, Kwamishina Maku ya sanar da takaita zirga zirgan ababen hawa daga karfe 8 na safe zuwa 2 na ranar Asabar. Daga karshe kuma ya bayyana godiyarsa ga jama’an jahar, sa’annan ya yi kira dasu kasance masu bin doka da oda, sa’annan su bayar da rahoton duk mutumin da basu fahimci take takensa ba.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Jigawa ta sanar da tura karin jami’an Yansanda zuwa karamar hukumar Guri domin kwantar da tarzomar da ta tashi a yankin wanda har ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin kabilun Hausawa da Fulanin yankin, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel