Ina bukatar a damko wadanda suka kai min hari a majalisar dattijai - Hadiza Bala Usman

Ina bukatar a damko wadanda suka kai min hari a majalisar dattijai - Hadiza Bala Usman

- Hadiza Bala Usman ta bukaci sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, shugaban majalisar dattijai da shugaban hukumar DSS da su binciko wadanda suka kai mata hari

- Ta bayyana yadda Idahosa Okunbo ya fusata a wajen taro a majalisar dattijai, hakan yasa 'yan daban da suka rakoshi kokarin cin zarafinta

- Sun yi ikirarin ba zasu kyaleta ba kuma zasu samota duk inda take matukar ta toshe musu hanyar cin abinci tare da Ubangidansu

Hadiza Bala Usman, manajan daraktan hukumar jiragen ruwa ta Najeriya, ta yi kira da cewa a binciki wasu mutane da take zargi da hantararta a farfajiyar majalisar dattijai.

A koken da ta mika ga sifeta janar din 'yan sanda, shugaban majalisar dattijai da kuma shugaban hukumar jami'an tsaro na fararen kaya, Usman ta yi bayanin zuwan da ta yi majalisar don amsa gayyatar da aka yi mata a majalisar.

Ta bayyana cewa, wasu mutane sun hareta wadanda take zargin hayarsu aka yi. Ta zargi Idahosa Okunbo, shugaban OMSL da wannan lamarin.

"A yayin taron, Kaftin Idahosa na OMSL, bayan ya yi bayaninsa, ya fita daga taron a harzuke kuma da matukar fushi," ta bayyana a kokenta.

DUBA WANNAN: Miyagu sun karbe kasa daga hannun Buhari - Aisha Buhari

Ta ce, "Bayan fitarsa, sai shugaban kwamitin hadin guiwar da ya gayyacemu majalisar ya rufe taron. Bayan fita daga dakin taron, wasu 'yan daba da suka rako Kaftin Idahosa sun biyoni har kofar fita kuma sun yi kokarin su tarar dani gaba da gaba. Sun zazzageni cewa ina toshe musu da ubangidansu hanyar cin abinci kuma zasu nemoni tare da tarwatsani."

Ta kara da cewa, kokarin jami'an tsaron da take tare da su ne tare da jami'an tsaron ofishin mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ta samu fita tare da tawagarta ba tare da sun cimma burinsu ba.

Ta ce yakamata a tuhumi Okunbo matukar wani abu mummuna ya faru da ita ko wani iyalinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel