Bayan kwanaki a boye, dan sandan da ya bindige direban mota ya mika kansa ga hukuma

Bayan kwanaki a boye, dan sandan da ya bindige direban mota ya mika kansa ga hukuma

Jami'in dan sandan da ya bindige direban mota don ya hanashi kudin goro a jihar Ondo ya mika kansa ga hukumar bayan an alanta nemansa ruwa a jallo.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Femi Joseph, ya alanta sunan dan sandan matsayin, Sajen Idowu Omosuyi.

SP Joseph ya ce Sajen Omosuyi ya mika kansa ga kwamitin binciken da kwamishanan yan sandan jihar ya nada ne ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba, 2019.

Yace: "Hukumar yan sandan jihar Ondo na farin cikin bayyanawa al'umma cewa jami'an dan sanda, Idowu Omosuyi, wanda ya bindige wani direba har lahira a Uso, ya mika kansa ga hukumar."

"Ya misa kansa ne da ranan nan (Alhamis) ga kwamitin binciken da kwamishanan yan sandan jihar yana don gudanar da bincike kan lamarin. Yanzu haka yana tsare a hedkwatar hukumar dake Akure."

"Wannan cigaban ba shakka zai taimaka mana wajen karkare bincikenmu cikin lokaci, sannan mu mika wanda ake zargin ga kotu."

"Muna sake jaddada cewa hukumar Sojin Najeriya ba za ta kare wani jami'inta da yayi ba dai-dai ba. ko ya saba doka."

Masu idanuwan shaida sun bayyana ainihin dalilin da yasa jami'in dan sanda ya bindige direban mota mai suna, Ado, a ranar Litinin yayinda ya nufi zuwa Abuja.

Daya daga cikin masu idon shaidan ya laburta cewa yan sandan na tsaye a kan titin Uso inda ya bukaci direban ya bada cin hanci amma ya ki saboda takardunsa sun cika kuma bai aikata wani laifi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel