Yanzu-yanzu: An kaiwa ministan Sufuri, Amaechi, hari a Madrid

Yanzu-yanzu: An kaiwa ministan Sufuri, Amaechi, hari a Madrid

Wasu matasan kungiyar yakin neman Biyafara IPOB mazauna kasar wajen sun kai wa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Chibuike Amaechi, hari a birnin Madrid, kasar Andalus.

Legit.ng ta samu labarin ne daga ministan da kansa inda ya bayyana cewa Allah ya kiyayeshi basu citar da shi kafin jami'an yan sanda suka cetoshi ba.

Ya tafi kasar Andalus halartan taron yakan canjin yanayi na duniya da ake gudanarwa a kasar.

Yace: "Wasu mintuna da suka wuce, wasu batattun yan Najeriya sun kawo min hari a taron yakan canjin yanayin da nazo halarta a Madrid, Spain.

"Jami'an yan sandan kasar Andalus sun kawar dasu kafin su cutar dani. Ina nan lafiya kuma ban samu rauni ba. Nagode da addu'o'inku da goyon baya.."

DUBA NAN Yanzu-yanzu: Bayan sakeshi jiya da dare, DSS ta lashi takobin sake damkeshi Sowore da safen nan

A watan Agusta, irin wannan abun ya faru da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, yayinda ya kai ziyara kasar Jamus.

Hakazalika hakan ya faru inda Matasan kasar Congo mazauna kasar Faransa suka suburbudi gwamnan jihar Kinshasha, Gentiny Ngobila Mbaka, wanda ya je yawon ganin ido kasar Faransa.

A bidiyon da ya bayyana a shafin ra'ayi da sada zumunta, an ga inda matasan ke jifansa da tutan kasar kuma suna watsa masa ruwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel