Dalilan da zasu sa Tinubu ya maye gurbin Buhari a 2023 - Hadimin Gbajabiamila

Dalilan da zasu sa Tinubu ya maye gurbin Buhari a 2023 - Hadimin Gbajabiamila

Abdullah Umar Farouk, babban hadimi ga kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila. Ya ce, kamata yayi jagaban jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya gaji Buhari a 2023 idan aka dubi irin gudumawar da yake badawa don habakar damokaradiyyar kasar nan.

Farouk ya zauna majalisar wakilai sau uku daga jihar Kebbi. Ya bayyana hakan ne a taron rantsar da kwamitin yada labarai na Tinubu a ranar Laraba a otal din Amana dake Abuja.

Ya ce, Tinubu ya nuna kwarewarsa a harkar shugabanci ta yadda ya sauya jihar Legas ta zamo birni mafi kyau a Afirka lokacin da yake gwamna. Ya ce hakan na nufin zai iya dasawa daga inda Buhari ya tsaya a shugabancin kasar nan.

DUBA WANNAN: Miyagu sun karbe kasa daga hannun mu - Aisha Buhari

Hadimin dan majalisar ya bayyana cewa, ba jihar Legas kadai Tinubu ya sauya ba, hatta kasar baki daya ya sauya. Ya tsaya tsayin daka wajen ganin karfin sojin kasar nan ya tabbata.

A bangaren mashiryin TMT 2023 na kasa, Muhammad Bello Doka, yayin jawabi a kan Tinubu ya san da wannan tafiya ko bai sani ba, ya ce: "Bai sani ba gaskiya. Amma mun kusa sanar dashi kuma ba zamu lamunci a'a ba a matsayin amsa ba. Zai fito takara sannan ya gyara mana kasarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel