Yanzu-yanzu: Buhari, Oshiomhole da shugabanin APC na jihohi sun shiga taro a Abuja

Yanzu-yanzu: Buhari, Oshiomhole da shugabanin APC na jihohi sun shiga taro a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari da shugabanin jam'iyyan All Progressives Congress (APC) na jihohin Najeriya sun shiga taro a babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban jam'iyyar ta APC na kasa, Mista Adams Oshiomhole shima yana cikin wadanda suka hallarci taron.

Oshiomhole ya iso fadar shugaban kasar kimanin karfe 11.30 na safe cike da kuzari duba da yadda ya amsa gaisuwar jami'an hukumar tsaro ta DSS da ke kofar shiga dakin taron kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wannan taron na zuwa ne kasa da sa'a 24 bayan Buhari da gwamnonin jam'iyyar ta APC sun gana a fadarsa a ranar Alhamis.

Ana tsamanin an kira taron ne domin warware wasu matsaloli da ke tasowa a jihar.

DUBA WANNAN: INEC ta tsayar da ranar maimaita zabukka 28 da kotu ta soke

A jihar su Oshiomhole, rikici ya barke tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki na jihar ta Edo kuma hakan ya rabba kan 'yan jam'iyyar suka gida biyu.

Tuni dai shugaban sashi jam'iyyar da ke biyaya ga Oshiomhole, Mista David Imuse ya isa wurin taron.

Sai dai shugaban jam'iyyar ta ke biyaya ga Obaseki, Mista Anselem Ojezuz bai iso wurin taron ba kafin a shiga taron na sirri.

An fara taron ne misalin karfe 12 na rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel