Atiku Abubakar ya zargi gwamnonin Najeriya da satar kudaden jahohinsu

Atiku Abubakar ya zargi gwamnonin Najeriya da satar kudaden jahohinsu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi gwamnonin jahohin Najeriya da karkatar da kudaden da aka basu domin cigaban ilimi a jahohinsu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Atiku ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a majalisar dattawan Najeriya inda ya je domin bayar da gudunmuwarsa tare da goyon bayan yunkurin samar da jami’ar Modibbo Adama a jahar Adamawa da kuma jami’ar kimiyyar noma a garin Funtua.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kwashe miliyoyin kudi bayan sun kashe ‘Dan canji’ a Abuja

Atiku ya yi kira ga majalisun dokokin Najeriya da su gudanar da gyare gyare a dokokin Najeriya ta yadda duk gwamnan jahar da aka kama ya karkatar da kudaden da aka tura musu domin cigaban ilimi ba zai sake samun wadannan kudi ba, sai dai a tura ma makarantun kai tsaye.

“Ina rokon yan majalis da su sakeyin duba ga wadannan dokoki, saboda banga dalilin da zai sa gwamna ya cinye kudaden da aka tura masa don cigaban ilimi a jaharsa ba, don haka akwai bukatar ku yi gyara a dokar ta yadda idan gwamna ya cinye kudin, sai gwamnati ta dinga tura kudaden kai tsaye ga jami’o’in.” Inji shi.

Idan za’a tuna a ranar Alhamis ne Atiku ya dira majalisar dattawan Najeriya domin halartar zaman sauraron korafe korafen jama’a game da kudurin sauya jami’ar kimiyya ta Modibbo Adama dake jahar Adamawa zuwa jami’ar komai da ruwanka.

Atiku yace idan aka sauya ma jami’ar Modibbo Adama matsayi, hakan zai bata daman gudanar da karatu a kan likitanci, kimiyyar hada magani, shari’a da dai sauransu.

An gudanar da wannan zama ne a dakin taro na 231 dake cikin majalisar dattawan, kuma Atikun ya halarci zaman ne a matsayinsa na dan jahar Adamawa, mai kishin jaharsa kuma mai ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Shi ma shugaban kwamitin kula da manyan makarantun gaba da sakandari da hukumar TETFund, Sanata Ahmad Kaita ya bayyana cewa makarantun idan an kafa su zasu taimaka wajen cigaban ilimin kimiyya a Najeriya

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel