Babu dan kudun da zai zama shugaban kasa a 2023 ba tare da Buhari ya taimaka masa ba - Rochas Okorocha

Babu dan kudun da zai zama shugaban kasa a 2023 ba tare da Buhari ya taimaka masa ba - Rochas Okorocha

- Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ja kunnen kabilar Igbo da ke fatan shugabancin kasar nan

- Ya bayyana cewa, kabilar ba zata taba shugabantar Najeriya ba sai da jagorancin wani sanannen dan Arewa

- Ya kwatanta 'yan Arewa musulmai da masu nagarta, imani , adalci da hadin kai

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltar jihar Imo ta Yamma, Sanata Rochas Okorocha ya yi bayani akan cewa dan kabilar Igbo ba zai taba hawa shugaban kasar nan ba a 2023, sai dai idan dan arewa ya taimaka.

A wata tattaunawa da aka yi da sanatan a Abuja, ya yi bayanin cewa Najeriya na bukatar shugaban kasa da zai tabbatar da tsaro, samar da aiyukan yi ga matasa tare da hada kan mutanen kasa.

Ya ce: "Kabilar Igbo kadai ba zasu taba iya shugabancin kasa ba. Zai fi kyau idan suka koma ba wa 'yan arewa da sauran yankunan kasar nan goyon baya. Hakan zai sa su cimma burinsu.

"Nasan zamu zo wajen wata rana, lokacin da za a shugabanci kasa ba don addini ko kabila ba. Amma matukar muka cigaba da taimakawa kabilanci da banbancin addinai, ba zamu ga dai-dai ba."

KU KARANTA: Dana sani keya ce: Matar da ta kashe makudan kudade domin ta zama namiji ta dawo tana so a mayar da ita mace ruwa a jallo

Okorocha ya jaddada cewa, kabilanci ko banbancin addinai bai kamata suna shiga siyasa ba, saboda talauci bai san kabila ko addini ba.

"Saboda kabila ba zata ciyar da mutum ba kuma ba zata bada tsaro ba."

"Kamar yadda kuka lura, siyasar kasar nan na hannun arewa ne saboda su ke da yawan kuri'u. Wani abu mai nagarta da na sani game da arewa shine, musulmai ne. Musulmi nagari kuwa yana da kyan halin adalci da hadin kai.

"Wannan kuwa shine burin da kowanne dan Najeriya na Kudu ke dashi. Zata kuma iya yuwuwa, adalcin Arewa ta sa su amincewa dan Kudu ya shugabanci Najeriya," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel