Sun taru su uku sun kashe mahaifinsu saboda fyade da yake yi musu kullum

Sun taru su uku sun kashe mahaifinsu saboda fyade da yake yi musu kullum

- Duk da cewa mahaifinsu ya dade yana lalata dasu tare da cin zarafi, 'yam mata biyu cikin ukun na fuskantar zargin kisan kai a Rasha

- Lauyoyi tare da kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam sun fito tare da kare 'yam matan da mahaifinsu ya dinga lalata dasu

- An gano cewa, sun yi amfani da barkono, wuka da kuma guduma wajen hallaka mahaifinsu mai suna Mikhail yayin baccinshi

Duk da yadda bincike ya nuna, tare da ganowa da aka yi 'yan uwa uku 'yam mata sun fuskanci cin zarafi ne daga mahaifinsu na tsawon shekaru, amma kotu tana tuhumar biyu daga ciki da laifin kisan kai.

Krestina na da shekaru 19, Angelina 18 sai Maria da ke da shekaru 17 sun hallaka mahaifinsu mai suna Mikhail ne da barkono, wuka da guduma yayin da yake bacci a watan Yuli na 2018. Sun yi hakan ne bayan shekaru da ya dauka yana cin zarafinsu.

Duk da cewa sama da mutane 364,000 suka sa hannu a kan koken kotu ta wankesu a wannan shekarar, kwamitin binciken kasar Rasha da ke kula da manyan laifuka, yace sai ya kammala bincike a kan biyu daga cikin 'yam matan. Akwai yuwuwar a garkamesu na shekaru 8 da kuma 20 bisa ga zargin da ake musu na kisan kai.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa

Kwamitin ya jaddada cewa, biyu daga cikin 'yam matan suna da hankali kuma sun san ma'anar abinda suka aikata. Kotun ta kushe ikirarin lauyoyi da masu rajin kare hakkin dan Adam da suka ce dole ne yasa 'yam matan suka cece rayuwarsu.

Za a mika karamar daga cikin 'yam matan zuwa asibitin kwakwalwa don samun kula.

Wannan ya biyo bayan bayanin da kotun rajin kare hakkin dan Adam ta Turai tayi, na cewa majalisar kasar Rasha bata yi bayani ko hukunta cin zarafi a cikin gida ba da babban laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel