Yanzu-yanzu: Bayan sakeshi jiya da dare, DSS ta lashi takobin sake damkeshi Sowore da safen nan

Yanzu-yanzu: Bayan sakeshi jiya da dare, DSS ta lashi takobin sake damkeshi Sowore da safen nan

Daga karshe, jami'an hukumar tsaron farin kaya wato DSS sun samu nasarar awon gaba da Omoyele Sowore da Bakare Mandate.

An tafi da su ofishin DSS.

Mun kawo muku rahoton cewa Jami'an DSS sun dira babbar kotun tarayya dake Abuja domin sake garkame Omoyele Sowore, Legit.ng Hausa ta tabbatar da hakan.

Jami'an DSS sun dira kotun ne da safiyar yau Juma'a inda suka fasa cikin kotun kuma suka fitittiki mutane.

Sahara Reporters ta bada rahoton cewa jami'an sun fitittiki Alkalin kotun, Jastis Ojukwu Ijeoma yayinda suka suburbudi wanda dan jarida.

Hukumar 'yan sandan farar hula ta Najeriya, DSS, a daren Alhamis ta sako Omoyele Sowore, mai wallafa jaridar Sahara Reporters.

An kama Mista Sowore ne tun a ranar 3 ga watan Augusta kan zarginsa da shirya zanga-zangan juyin juya hali tare da neman gwamnati ta zage damtsen ta wurin kyautatawa 'yan kasa.

Mista Sowore ya cika ka'idojin belinsa a ranar 6 ga watan Nuwamba, misalin wata guda da ta shude kenan amma ba a sako shi ba. Wani alkalin kotun tarayya, a safiyar Alhamis ya bayar da wa'addin awanni 24 don a saki Mista Sowore.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel