Majalisa za ta fara gyaran kundin tsarin mulki a Janairun 2020 - Lawan

Majalisa za ta fara gyaran kundin tsarin mulki a Janairun 2020 - Lawan

A jiya ne shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan ya bayyanawa majalisar dalilin da yasa ba a kafa kwamitin kara duba kundin tsarin mulki ba. Yace a wata mai zuwa za a fara wannan aiki. An barshi zuwa wata mai zuwa ne saboda lamurran kasafin kudin shekarar 2020 da ya sha kan 'yan majalisar.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da jakadan kungiyar hadin kan Turai a Najeriya da ECOWAS, Ketil Karlsen wanda ya kai masa ziyara

Ya kara da tabbatarwa da kasar cewa, za a kafa kwamitin nan ba da dadewa ba.

"Nan ba da dadewa ba za a kafa kwamitin duba kundin tsarin mulkin kasar nan. Ba mu yi hakan ba har yanzu saboda akwai wasu al'amura da suka sha mana kai. Bayan an gama da harkar kasafin kudin 2020. Nan da watan Janairu na 2020, kwamitin zai fara aikin," in ji Lawan.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Ya sanar da bakonsa cewa akwai niyya tare da burin kara duba kundin tsarin mulkin kasar nan.

Lawan ya bayyana godiyarsa game da goyon bayan da EU ke ba Najeriya ballantana a bangaren zabe da cigaban siyasa a kasar nan.

"Tun a 1999, damokaradiyyarmu ta samu goyon baya daga EU kuma hakan na bada gudummawa mai kyau. Alakar da ke tsakanin EU da gwamnatin Najeriya ba kamar irin wacce ta ke tsakanin kungiyoyi bace."

Lawan ya bukaci EU da ta cigaba da tallafawa Najeriya a bangarori irinsu INEC, tsarin kasa da kudi.

Ambasada Karslen ya bayyana cewa, shugabancin EU din zai tabbatar da an kara dankon alaka tare da dangantaka mai kyau tsakaninta da Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel