Yan bindiga sun kwashe miliyoyin kudi bayan sun kashe ‘Dan canji’ a Abuja

Yan bindiga sun kwashe miliyoyin kudi bayan sun kashe ‘Dan canji’ a Abuja

Wasu gungun yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai farmaki kasuwar yan canjin dala dake Zone 4 a babban birnin tarayya Abuja inda suka kashe wani hamshakin dan canji, sa’annan suka yi awon gaba da makudan kudade.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaitp lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis a lokacin da yan canjin suka fara harkokinsu. Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyar Legit.ng sunan mamacin Hamisu Naira.

KU KARANTA: Alaramma da ya amshi naira biliyan 1 don cusa haddar Qur’ani a kan wani ya shiga hannun EFCC

“Yan fashin sun yi basaja ne kamar zasu yi canjin kudi, inda suka kira Hamisu Naira, zuwansa keda wuya suka kwace jakar Ghana-Must-Go dake hannunsa dake makare da naira, daloli, fam da yuro yuro, amma Hamisu Naira ya rike jakarsa gam! Ya ki saki.

“Hamisu ya rike jakar kudin ne saboda ba kudinsa bane kadai, amma ganin yadda ya tubure sai yan bindigan suka dirka masa harsashi suka tsere da jakar. Harbin ya ja hankalin kowa a cikin kasuwar, sai dai ganin gawar Naira muka yi kwance cikin jini.

“Ba tare da bata lokaci ba wasu yan kasuwan suka dauke gawar mamacin da gaggawa, sa’annan suka sanar da Yansanda.” Inji shi.

Daga karshe an gudanar da jana’izar Hamisu kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanada. Majiyar ta kara da cewa Hamisu dan asalin garin Hadejia a jahar Jigawa ne.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wasu miyagun mutane biyu da ake zargi da satar mutane tare da yin garkuwa dasu, ta hanyar banka musu wuta da wasu fusatattun matasa suka yi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Asinim Butswat ya bayyana cewa a ranar Talata, 3 ga watan Disamba aka kama masu garkuwan, amma jim kadan bayan Yansanda sun kamasu ne sai matasan yankin suka kwacesu daga hannunsu, nan take suka banka musu wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel