Kwamitin shari’a zai nemi tsige Donald Trump daga mulki – Pelosi

Kwamitin shari’a zai nemi tsige Donald Trump daga mulki – Pelosi

Gidan Jaridar NBC sun rahoto cewa kakakin majalisar wakilan tarayya na kasar Amurka, Nancy Pelosi, ta sanar da cewa za su fara shirin sauke Donald Trump daga kujerar shugaban kasa.

Nancy Pelosi ta bada wannan sanarwa ne a Ranar Alhamis, 5 ga Watan Disamban 2019, ta na mai cewa ta umarci kwamitin shari’a ta majalisar tarayya su fara tattara takardun tsige shugaban.

Kakakin majalisar ta yi wannan bayani ne a wani gajeren bidiyo da ta fitar ta na mai magana kai-tsaye da mutanen Amurka. Yanzu haka wannan bidiyo ya karada Duniya, ya jawo maganganu.

Shugabar majalisar ta nuna cewa matakin da ta dauka abin bakin ciki ne amma ya zamana dole ba tare da nuna girman kai ba sai domin biyayya ga Iyayen gida da mutanen kasar ta Amurka.

Pelosi ta ke cewa: “Ina sanar da shugabanninmu su fara maganar tsige shugaban kasar.” Kakakin majalisar ta ce ta tabbata Trump ya wuce gona da iri tare da sabawa dokar kasar a kan kujerar.

KU KARANTA: Buhari ya taya Kaigama murnar nadin da Fafaroma ya yi masa

Majalisar ta bayyanawa Duniya cewa shugaba Donald Trump ya jefa sha’anin tsaron Amurka a cikin matsala ta hanyar janye gudumuwar Sojin da su ka saba ba Ukraine, saboda siyasarsa.

Nancy Pelosi ta jefi shugaban kasar da zargi mai karfi da yin wani taro da kasar Ukraine saboda binciken wani ‘Dan adawarsa. A cewar ta wadannan sun sabawa kundin tsarin mulkin Amurka.

A kokarin cin zabe ko ta wani irin hali, Pelosi ta fadawa Masana tsarin mulki cewa Trump ya karya rantsuwar da ya dauka na shiga ofis na cewa zai bi kundin tsarin mulki sau da kafa.

Idan ba ku manta ba, wannan kwamiti da ke binciken shugaban kasar ya bayyana cewa ya na da tulin hujjojin da za su sa a tsige shugaban daga ofis. Trump ya dade ya na watsi da wannan zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel