Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi ya fi alkhairi - Sheikh Daurawa

Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi ya fi alkhairi - Sheikh Daurawa

- Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin mutanen jihar

- Daurawa ya ce, a tunaninsu barin kirkirar sabbin masarautun nan a jihar Kano zai fi zama alheri

- A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da kirkirar sabbin masarautun

Sanannen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin mutanen jihar kafin kirkirar sabbin masarautun.

A tattaunawar da Shehin malamin ya yi da Hausa RFI, ya ce suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi zai fi alheri, don kauce wa wargaza kawunan al'umma.

Sai dai kash! A ranar Alhamis ne majalisar jihar Kano din ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautun. Hakan ya biyo bayan gabatar da kudirin da Ganduje ya kara yi a gaban majalisar a ranar Litinin da ta gabata.

Bayan an karanta bukatar kashi na uku a ranar Alhamis, majalisar ta amince da hakan ya zamo doka a jihar. Duk kuwa da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.

KU KARANTA: Babbar magana: Ya kamata a halatta yin fyade, kuma mata su dinga bada hadin kai a lokacin da ake yi musu - Cewar wani jarumin fim

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar kuma sun dau matakin domin talakawa ne.

A shekarar da ta gabata ne, Gwamna Ganduje ya kirkiro da sabbin masarautun, lamarin da ya ja ake kallon za a rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Sabbin masarautun sune: Bichi, karkashin Aminu Bayero; Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila; Karaye, karkashin Ibrahim Abubakar sai kuma Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel