Babbar magana: Ya kamata a halatta yin fyade, kuma mata su dinga bada hadin kai a lokacin da ake yi musu - Cewar wani jarumin fim

Babbar magana: Ya kamata a halatta yin fyade, kuma mata su dinga bada hadin kai a lokacin da ake yi musu - Cewar wani jarumin fim

- Wani dan fim mai suna Shravan Daniel ya nemi gwamnatin kasar Indiya da ta halatta fyade

- Ya yi kira ga mata da su dinga bada hadin kai yayin fyade tare da tafiya da kwaroron roba don ko ta kwana

- Ya yi wannan bayanin ne bayan da wani mutum ya hallaka wata budurwa da ta taimaka mishi ta hanyar yi mata fyade

Wani dan fim yace fyade ba wani babban lamari bane, kuma kamata yayi mata su dinga bada hadin kai a yayin da ake musu fyade.

Daniel Shravan, dan fim din Indiya ya yi wannan maganar ne mai cike da abun mamaki, yayin da yake mayar da martani a kan mutuwar Priyanka Reddy.

Budurwar mai shekaru 27 ta rasa ranta ne bayan da wanda ta taimakawa ya yi mata fyade yayin da tayar motarta ta sace. An samu gangar jikinta ne a karkashin gada kusa da Hyderabad a Indiya cikin makon da ya gabata.

Bayan mutuwar budurwar, Daniel Shravan ya yi kokarin yin bayani a kan cewa a halasta harin jima'i da ba ta karfin tsiya ba. Ya ce, kamata yayi mata su dinga yawo da kwaroron roba don shiryawa fyade, kuma su bada hadin kai mai yawan gaske ga masu fyaden.

KU KARANTA: Sharik Tobar: Kyakkyawar budurwar da take shafe wata biyu cur tana bacci ba tare da ta tashi ba

Daniel Shravan ya ce: "Fyade ba wani babban abu bane, kisa ce dai bai kamata a bata uziri ba."

Ya kara da cewa, "kamata yayi gwamnati ta halatta fyade amma na lumana."

Shravan yace ana kashe matan ne saboda kokarin fada da sukeyi ko illata masu fyaden. Ya kara da cewa ana kashe matan ne saboda fusatar da suke nunawa bayan an kammala fyaden.

Ya ce: "Masu yin fyade na samun hanyar fitar da sha'awarsu ne. Kuma ana kashe matan ne saboda damuwar da suke nunawa. Zai fi kyau idan mata suka karba fyade da hannu bibbiyu."

Ya kara da cewa, kamata yayi matan Indiya su san ilimin jima'i kuma su dinga yawo da kwaroron roba don ko ta kwana.

Shravan ya kara da cewa, gwamnatin kasar Indiya na tsorata masu fyade. Ya ce dokokin da ke sa a hukunta masu fyade bayan wadanda suka yiwa fyaden sun kai kara, ke sa a kashe wadanda aka yi wa fyade.

Tuni dai aka dinga kushewa da caccakarsa a kan wannan abu da ya wallafa. Babu dadewa kuwa ya goge rubutun bayan da mutane suka ce zasu kauracewa fina-finanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel