Yanzu-yanzu: Everton ta fatattaki manajanta, Marco Silva

Yanzu-yanzu: Everton ta fatattaki manajanta, Marco Silva

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallami manajan ta Marco Silva bayan mummunan kayen da ta sha a hannun Liverpool a Merseyside derby.

Rashin nasarar da Everton ta yi a rannar Laraba ya saka kungiyar ta koma rukunnin kungiyoyin da ba za su samu damar buga gasar cin manyan kofunan kakkan wasa mai zuwa ba hakan yasa mahukunta kungiyar suka dauki matakin sallamarsa.

Everton ta lashe wasanni hudu ne kacal cikin 15 da ta buga a Premier League na bana amma irin mummunan kayen da suka sha a hannun makwabtansu ranar Laraba ya nuna cewa wa'adin Silva ya zo karshe a kungiyar.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

An ruwaito cewa direktan kwallo, Marcel Brands da babban jami'n kudi na kungiyar Alexander Ryazantsev suna ta nuna alamun bacin rai a Anfield yayin da magoya bayan kungiyar suka fara ficewa tun kafin a tashi wasar a Stanley Park.

Silva ya bi bayan wanda ya gabace shi wato tsohon manajan Everton Ronald Keoman da aka sallama bayan kungiyar ta sha kaye a hannun Arsenal a watan Oktoban 2017 inda aka tashi wasar 5-2.

Matakin da kungiyar da dauka a yau ta sawake wa Silva muwuyacin halin da ya shiga na tsawon makonni kan makomarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel