Ina taya ka murnar zama Jagoran Katolika – Buhari ya fadawa Ignatius Kaigama

Ina taya ka murnar zama Jagoran Katolika – Buhari ya fadawa Ignatius Kaigama

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika takarda ta musamman domin taya murna ga Ignatius Kaigama. Hakan na zuwa ne bayan an nada Malamin a matsayin Jagoran Garin Abuja.

Bishof Ignatius Kaigama ya zama babban Limamin katolikan Lardin Abuja ne kwanan nan. Wannan ya sa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya aika sakonsa domin taya sa murna.

Jawabin shugaban kasar ya fito ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, a Ranar Alhamis, 5 ga Watan Disamban 2019. Shugaban kasar ya ce ya na yi wa Malamin Allah taya-riko.

Matsakaicin jawabin shugaban kasar ya fara ne da cewa: “Ina taya ka murnar nada ka da Fafaroma Pope Francis, ya yi a matsayin babban Limamin Darikar katolika na yankin Abuja”

A wannan jawabi da ya fito Ranar 5 ga Disamba, Buhari ya ce: “Duba da irin tarihin ka a matsayin Malamin addini, kuma shugaba, na tabbata cewa za ka yi namijin kokari a sabon ofishin na ka.”

KU KARANTA: An kubutar da wasu Bayin Allah daga hannun 'Yan ta'adda

Shugaban kasar ya lissafo aikin da Malamin ya yi ba da dadewa ba a kujerar shugaban kungiyar Fastocin Katolikan Najeriya, da kuma Limamin Garin Jos, da shugaban wata kungiya ta Afrika.

Bayan haka Kaigama ya rike mukamin shugaban kwamitin hadin-kan addinai na zaman lafiya a Filato, duba da wadannan, Buhari ya ce sabon shugaban Mabiya Katolikan ba zai bada kunya ba.

“Ka saba yunkurin kawo zaman lafiya, da shirya taron hadin-kai da fahimtar juna tsakanin addinai. Ina yi maka fatan alheri a matsayinka na Jagoran Mabiya Darikar Katolika na Abuja.”

Shugaban na Najeriya ya kare sakon murnar ta sa da cewa: “Ina taya ka murna!” Haifaffen Jihar Taraban, ya gaji John Onaiyekan ne wanda ya yi ritaya daga aiki bayan ya cika shekara 75.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel