Yanzu-yanzu: DSS ta sako Omoyele Sowore

Yanzu-yanzu: DSS ta sako Omoyele Sowore

Hukumar 'yan sandan farar hula ta Najeriya, DSS, a daren Alhamis ta sako Omoyele Sowore, mai wallafa jaridar Sahara Reporters.

An kama Mista Sowore ne tun a ranar 3 ga watan Augusta kan zarginsa da shirya zanga-zangan juyin juya hali tare da neman gwamnati ta zage damtsen ta wurin kyautatawa 'yan kasa.

Mista Sowore ya cika ka'idojin belinsa a ranar 6 ga watan Nuwamba, misalin wata guda da ta shude kenan amma ba a sako shi ba. Wani alkalin kotun tarayya, a safiyar Alhamis ya bayar da wa'addin awanni 24 don a saki Mista Sowore.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

Lauyan Mista Sowore, Femi Falana yayin tabbatarwa Premium Times ya ce hukumar ta DSS ta biya Sowore tarar N100,000 kamar yadda alkaliyar kotun Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ya bayar da umurni.

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

Falana ya ce an sako su ne misalin karfe bakwai na yamma

Ya ce, "an sako shi kimanin mintuna 30 da suka wuce. Sun mika shi hannun wani daga cikin lauyoyin mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel